Daga MUHAMMAD AL-AMIN a Damaturu
Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da Talata, 15 ga Yuli, 2025, ta kasance ranar hutu domin yin jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadi a wani asibiti da ke birnin Landan.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna Buni, Mamman Mohammed, ya fitar ta buƙaci ma’aikata da ɗaukacin al’ummar jihar da su ɗauki wannan rana wajen yin addu’o’i na musamman ga marigayi, shugaba Muhammadu Buhari.
Gwamnan ya buƙaci limamai a jihar su yi amfani da ranar wajen gudanar da addu’o’i a masallatai domin marigayin da kuma ƙasa baki ɗaya.
“Shugaban ƙasa ya taka
muhimmiyar rawa wajen
kawo ci gaba da zaman lafiya a Jihar Yobe da Arewa
maso Gabas gaba ɗaya. Ya cancanci wannan
girmamawa daga mutanen jihar,” in ji Gwamna Buni.
A hannu guda kuma, majalisar zartarwar jihar ta gudanar da taron addu’a na musamman a maimakon zaman mako-mako wanda take, domin girmama marigayin tsohon shugaban ƙasa.
Tun da farko, a cikin saƙon ta’aziyyarsa, Gwamna Buni ya bayyana Buhari a matsayin gwarzon ɗan kishin ƙasa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da haɗin kai da ci gaban Nijeriya.
Gwamnan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki ya gafarta masa, ya sa Aljannah Firdausi ce makomar sa.
A ƙarshe, Gwamna Buni ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, iyalan marigayin, gwamnatin Jihar Katsina, masarautar Daura da ɗaukacin al’ummar Nijeriya kan wannan babban rashi da ya girgiza ƙasa baki ɗaya.
