Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wannan bayanin na ƙunshe ne a wata takardar sanar ɗauke da sa hannun babban jami’in hulɗa da jama’a na gwamnan Katsina Muhammadu kaula.
Yanzu ana sa ran isowar gawar marigayi Muhammadu Buhari gobe talata da ƙarfe 12 na rana.
Haka kuwa ya biyo bayan cimma matsaya tsakanin gwamnatin Katsina da iyalan marigayi Muhammadu Buhari.
Mutane da ƙungiyoyi ke ta miƙa saƙon ta’aziyar su ga gwamnatin da iyalan marigayi Muhammadu Buhari.
