Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar gwamnonin Arewa maso Yamma sun ce sun ɗimauta da juyayin rasuwar tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari.
A wata takarda ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Katsina malam Dikko Raɗɗa ya bayyana rasuwar Muhammadu Buhari a matsayin babban rashi ga al’ummar Jihar Katsina da jihohin Arewa maso Yamma dama ƙasa baki ɗaya.
Ƙungiyar sai ta ayyana gobe talata a matsayin hutu ga al’ummar jihohin domin girmama tsohon shugaban ƙasar.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ce a madadin gwamnonin Arewa maso Yamma yana miƙa ta’aziya ga iyalan tsohon shugaban ƙasar, al’ummar Jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya da fatan Allah masa rahama, ya yafe masa kurakuransa, ya sa aljannah Firdausi ce makomar sa.
Ana sa ran kawo gawar sa gobe Talata da ƙarfe 12 na rana Sannan ayi jana’izar sa da ƙarfe 2 na yamma a garin Daura inda nan ne mahaifarsa.
