Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Katsina ya bayyana rasuwar shahararren mawaƙin Muhammadu Buhari wanda aka fi sani da Kosan Waƙa a matsayin babban rashi ga ƙungiyar mawaƙan Hausa.
Kosan Waka ɗan asalin ƙaramar hukumar Batagarawa a Jihar Katsina ya rasu yana da shekara 47 da haihuwa.
A wata sanarwa ɗauke da sa hannun mai magana da yawun gwamnan, Muhammadu Kaula, Gwamna Raɗɗa ya bayyana Kosan Waƙa a matsayin mutumin kirki wanda yawancin waƙoƙin sa na ilmantarwa,da fadakarwa kan mahimmancin zaman lafiya.
“Waƙoƙin sa na isar da saƙon zaman lafiya, ɗaukaka al’adunmu, ilmantar da al’umma akan siyasa da gwamnatin.Yana ɗaya daga cikin mawaƙan da su ke burge ni tuni lakacin da nake riƙe da muƙamin DG SMEDEN,”Inji Raɗɗa.
Ya bayana cewa marigayi Kosan Waka yana halartar duk wani taron biki da Gwamnatin Katsina ke shirya wa kuma ta gayyace sa inda ya kan yaɗa buƙatar zaman lafiya a tsakankanin al’umma.
Malam Dikko Raɗɗa ya bayyana mutuwar Kosan Waka a matsayin babban rashi ga al’ummar Jihar Katsina da masana’antar waƙa,yayi addu’ar Allah yafe masa kurakuran sa ya sanya aljanna fiddausi ne makomar sa.
Kosan Waka ya rasu a wata asibiti da ke Kano bayan ya yi fama da rashin lafiya.
