Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Ƙungiyar Miyetti Allah reshen ƙaramar hukumar Augie da ke jihar Kebbi ta ce ta ja ɗamarar yaƙi da ‘yan ci da ceto a yankin.
Alhaji Rugga Shehu shugaban ƙungiyar na ƙaramar hukumar Augie ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da waƙilin jaridar Blueprint Manhaja a garin Augie ƙarshen makon nan.
Alhaji Rugga Shehu ya ce lokaci ya yi da za a hana duk wani mutum shiga tsakanin fulani da hukuma idan wata shari’a ta samu saboda sau da yawa waɗansu fulani suna shiga tsakani da sunan ƙungiyar Miyetti Allah suna tatsar kuɗi daga fulani da sunan daidaitawa ko sasantawa.
Ya ƙara da cewa Fulani sun daɗe suna shan wahala hannun waɗannan mutanen ‘yan ci da ceto masu da’awar shugabancin ƙungiyar Miyetti Allah inda a duk lokacin da wata Shari’a ta samu musamman tsakanin su da manoma haka za su yi ta tatsar kuɗi daga hannun su kuma lamarin ya ƙi ci ya ƙi cinyewa wanda da tsakanin su ne da abokan shari’ar su ne abin ba zai kai hakanan ba.
Ya ce daga yanzu duk wanda wata matsala ta shari’a ta taso ba wani da zai je da sunan ƙungiyar Miyetti Allah sai ta hanyar tsarin da aka yi yanzu kuma ƙungiyar za ta ɗauki matakin ladabtarwa ga duk wanda ya taka wannan dokar.
Ba za mu ƙyale waɗansu ɓara-gurbi daga cikin mu da kuma hausawa suna haɗa baki suna cin amanar mutane ba. “Inji shi”
