
Daka ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya shaida wa manema labarai haka a garin Daura, a lokacin da ya je duba shirye-shiryen da aka yi na gudanar da jana’izar marigayi Muhammadu Buhari.
Gwamnan ya ce, iyalan marigayin sun shaida masa cewa marigayin ya bar wasiyyar cewa idan ya mutu a rufe shi a gidansa na Daura.
Haka kuma, Raɗɗa ya ce za a yi jana’izar sa mamacin ne a filin Kangiwa da ke Fadar Sarkin Daura bisa shawaran jami’an tsaro.
Daga ƙarshe, Gwamnan ya kirayi al’ummar garin Daura da su bada haɗin kai wajen gudanar da hidimar jana’izar cikin kwanciyar hankali domin a cewarsa daga cikin baƙin da za su halarci jana’izar har da na ƙasashen waje.
Ana sa ran Shugaban Bola Tinubu da wasu shugabannin ƙasashe biyu za su je jana’izar.
