Sojoji sun daƙile yunƙurin garkuwa na Boko Haram, sun ceto fararen hula 31 a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro na Atisayen Haɗin Kai a Arewa maso Gabas sun yi nasarar daƙile wani harin ‘yan ta’adda na yunƙurin garkuwa, inda suka ceto mutane 31 a atisayen, wanda aka ƙaddamar a yankin titin Buratai zuwa Kamuya da ke Ƙaramar Hukumar Biu a Jihar Borno.

Atisayen ya kuma yi sanadiyyar ƙwato motocin fararen hula guda huɗu da baburan da ‘yan ta’addar suka tsere suka bar su bayan musayar wuta a tsakanin ɓangarorin biyu.

Jam’in yaɗa labaran sojojin na riƙo, Kyaftin Mohammed Goni ne ya sanar da ci-gaban a wata takarda da ya fitar, inda ya ce al’amarin ya auku ne a ranar Juma’a, 31 ga watan Yulin 2026.

A cewar sanarwar, dakaru na musamman na Bataliya ta 135 da ke Dutsen Kura ne suka bi diddigin zirga-zirgar mayaƙan Boko Haram/ISWAP ɗin a lokacin da suke bincike da mislain ƙarfe 3:45 na yamma, lamarin da ya sa cikin hanzari suka farmake su a lokacin da suke tafiya da mutanen da suka sacen.

Al’amarin ya faru ne bayan bataliyar ta gaggauta tura jami’ai, inda suka cimma ‘yan ta’addar a lokacin da suke yankin Mangari zuwa Dora.

Ya bayyana cewa, ƙarfin makamai da ƙwarewar aiki daga ɓangaren dakarun tsaron sun taimaka wajen kora ‘yan ta’addar, lamarin da ya sa suka tsere ba shiri tare da barin motoci da mutanen da suka sacen.

Haka kuma, Kyaftin Goni ya ce sojojin sun ƙwato baburan da mayaƙan watsar yayin tserewar a lokacin atisayen. Ya bayyana cewa, babu ɗaya daga cikin fararen hular da aka cutar ko aka lalata wa abin hawa.

A ƙarshe, ya jaddada aniyar rundunar sojin ta cigaba da aiki tuƙuru wajen ƙaddamar da ire-iren atisayen da nufin daƙile ayyukan ta’addanci tare da bayar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’umma a shiyyar da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji

Leave a Reply