Shugabar jam’iyyar LP ta yi kira da a yi zaɓen 2027 cikin lumana

Spread the love

Daga AHMID LAWAL a Abuja

Shugabar Jam’iyyar LP Sanata Nenadi Usman, ta yi kira ga shugabannin siyasa da su ajiye ƙiyayya, su kuma tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya kasance gasa ta ra’ayoyi ba yaƙi ba.

Usman ta yi wannan jawabi ne a Jos, babban birnin Jihar Filato, yayin bikin cika shekara 80 da haihuwa na tsohon Gwamnan Jihar Filato da tsohuwar Jihar Benue, Sanata Jonah David Jang, jiya.

Wannan jawabi ya fito ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar a ƙasa, Ken Asogwa, ya fitar a Abuja, ranar Asabar.

Asogwa yace shugabar jam’iyyar tace, makomar Najeriya tana dogara ne akan ko ‘yan siyasa za su iya ɗaga ƙasar sama da jam’iyya da son zuciya.

Shugabar LP ta yi gargaɗi kan maganganun da ka iya tayar da hankali, inda ta ce saɓani na siyasa bai kamata ya rikiɗe ya zama abota da gaba tsakanin ‘yan ƙasa ba.

Ta ce, “Jam’iyyunmu na siyasa na iya bambanta, amma ƙasarmu ɗaya ce.
Muna da alhakin tabbatar da siyasa ba tare da rushe zumuncin da ke ɗaure ƙasarmu ba” A cewar ta.

Sanata Usman ta bayyana Sanata Jang a matsayin ɗan kishin ƙasa wanda shekaru da dama na hidima a soja da siyasa suka ba shi matsayi a tarihin Najeriya.

Ta ce, rayuwar Jang ta nuna ladabi, jarumtaka da sadaukarwa, tun daga matsayin soja har zuwa Gwamnan Jihar Filato da kuma Sanata a Majalisar Ɗinkin Najeriya.

By ukarofi

Leave a Reply