Gwamna Raɗɗa ya yi kira ga al’ummar jihar su guji siyasantar da matsalar tsaro

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da yin addu’o’in zaman lafiya, su mara wa jami’an tsaro baya, tare da kauce wa masu amfani da matsalar tsaro wajen cimma muradun siyasa.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin bikin Yaumul Shukur 2026, bikin godiya na shekara-shekara da ake gudanarwa domin tunawa da haɗewar tsoffin Lardunan Katsina da Daura a shekarar 1934.

Gwamna Raɗɗa ya ce tabbatar da tsaro alhakin kowa ne, kuma bai kamata a mayar da shi batun siyasa ko son zuciya ba.

“Wannan ba taro ba ne kawai. Al’ada ce ta godiya da iyayenmu suka assasa. Shi ya sa a kowace ranar 1 ga Agusta muke gudanar da Yaumul Shukur domin gode wa Allah tare da roƙon Ya ci gaba da kare jiharmu.”

Gwamnan ya bayyana Jihar Katsina a matsayin jiha mai albarka, yana mai yabawa irin gudunmawar da ‘ya’yanta ke bayarwa a cikin gida da ma ƙasashen waje.

Haka kuma ya karrama tsoffin shugabannin ƙasa, Marigayi Umaru Musa Yar’Adua da Marigayi Muhammadu Buhari, tare da fitattun alƙalai da malamai daga Katsina da Daura, ciki har da Justice Muhammadu Bello, Justice Mamman Nasir da Justice Umaru Abdullahi, da sauran manyan malamai da suka yi fice wajen tabbatar da gaskiya da adalci.

Gwamna Raɗɗa ya jaddada cewa gwamnatoci na zuwa su wuce, amma Jihar Katsina za ta ci gaba da wanzuwa, don haka wajibi ne kowa ya ba da gudunmawarsa wajen kare ta.

“Mun ɗauki aiki, mun horas tare da tanadar wa Rundunar Katsina State Community Watch Corps kayan aiki domin ta taimaka wa jami’an tsaro na hukuma. Za mu yi amfani da duk hanyoyin da doka ta amince da su wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”Inji Dikko Raɗɗa.

Gwamnan ya yabawa rundunar sojoji, ‘yan sanda da jami’an Community Watch Corps bisa haɗin gwiwar da suka yi a hare-haren baya-bayan nan, waɗanda suka yi sanadin kashe sama da ‘yan bindiga 40, ciki har da wani fitaccen jagoransu.
Ya kuma gargaɗi masu amfani da mutuwar bayin Allah wajen neman ribar siyasa.

“Kada wani ya yi amfani da mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba domin neman mulki. Rayuwar ɗan Adam mai tsarki ce, kuma tsaro dole ne ya kasance abin da ya fi komai muhimmanci.”

Gwamna Raɗɗa ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya, malamai da sauran al’umma da su ci gaba da yin addu’o’in samun zaɓe cikin lumana, haɗin kai da ci gaban Jihar Katsina.

Tun da farko, Kwamishinan Harkokin Addini, Alhaji Ishaq Shehu Dabai, da Shugaban Kwamitin Shirya Taron, Khadi Ahmed Muhammad, sun bayyana cewa bikin Yaumul Shukur wani lokaci ne na gode wa Allah tare da ƙarfafa al’umma su ci gaba da mara wa gwamnati baya a ƙoƙarin tabbatar da tsaro da walwalar jama’a.

Shi ma Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya buƙaci al’umma da su kiyaye da kuma ci gaba da gina gadon haɗin kai da ‘yan’uwantaka da suka gada daga magabatan Katsina da Daura.

Bikin ya samu halartar Mataimakin Gwamna, Malam Faruk Lawal Jobe; Kakakin Majalisar Dokokin Jihar, Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura; Sakataren Gwamnatin Jiha, Abdullahi Garba Faskari; Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jiha, Alhaji Falalu Baale; Shugaban Ma’aikatan Gwamna, Alhaji Abdulkadir Mamman Nasir; mambobin Majalisar Zartarwa ta Jiha; Sakatarorin Dindindin da sauran manyan jami’an gwamnati.

By ukarofi