Masu fassarar finafinan Indiya na buƙatar tallafin gwamnati – Shugaban ƙungiyar Auwal Badi

Spread the love

“kaso 95 cikin masu harkar fassarar fim matasa ne”

Daga MUKHTAR YAkUBU

Harkar fassarar finafinan Indiya da kasuwancin sa wata babbar hanya ce da dumbin matasan mu musamman na Arewa suka dogara da ita wajen tafiyar da rayuwarsu ta yau da kullum. 

A yanzu wannan harka ta fassarar finafinan Indiya da kasuwancin sa tana ɗaya daga cikin manyan kasuwancin da take samar wa matasa aikin yi. kuma hakan ya taimaka wajen samun hanyar dogaro da kai ga matasa sama da miliyan ɗaya a faɗin ƙasar nan.

Ganin irin kallon da ake yi wa Ita harkar da kuma yadda gwamnati ba ta bata kulawar da ta dace duk da tana samun kuɗaɗen shiga daga harkar ne ya sa muka tattauna da shugaban ƙungiyar na ƙasa Auwal Badi domin jin yadda suke gudanar da harkar da kuma irin tallafin da suke son su samu daga gwamnati domin bunƙasa kasuwancin na su. Don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

MANHAJA: Da farko za mu so ka gabatar da kanka ga masu karatun mu.

AUWAL BADI: To ni dai sunana Auwal Badi, kuma ni ne Shugaban ƙungiyar Masu fassarar Finafinan Indiya da kasuwancin na kasa.

To ko za ka yi mana bayani dangane da ƙungiyar ta masu fassarar finafinan Indiya da kasuwancin a ɗan takaici?

To Ita wannan ƙungiyar ta masu kamfanonin fassarar finafinan Indiya ce da kuma kasuwancin sa. Kuma Ita wannan ƙungiyar ta kasa ce, duk wanda yake kasuwanci da fassarar finafinan Indiya da kasuwancin sa, to yana ƙarƙashin ƙungiyar ne. Ta hannun mu masu tarawa a waya suke saya su tura wa mutane don haka duk tafiyar mu ɗaya da su sai da su za mu yi harkar, kuma su ma sai da mu za su yi harkar. Sannan kaso 95 cikin masu wannan harkar duk matasa ne wadda ta haka ne suka samu sana’ar yi suke rike da kansu da iyayensu, wasu suna da aure ma. Don a yanzu za iya cewa da kai a wannan harkar tamu za a samu matasa sama da miliyan biyu da suke cin abinci a cikin ta, kuma hakan ya rage raɗaɗi na zaman banza , ya zama cewa an yaƙi talauci. Matasa sun samu sana’ar yi wani ya yi aure wani ya mallaki gida, kai har masu motoci ma akwai.

Kamar yadda ka ce ƙungiyar ta tara matasa ne kashi 95 cikin dari. Ko ya ya harkar gudanar da ƙungiyar yake tafiya?

To Alhamdulillah, ai mu muna da fahimtar juna sosai kuma al”amuran mu suna tafiya, tun da mu a matsayin mu na shugabanni na ƙasa duk inda muka je wani gari ko da ba ka san shugaban da yake gudanar da shugabancin tura finafinai a garin ba, idan ka je zai gabatar da kansa ne saboda mun zama ɗaya mu da su, sai muke ɗaukar kanmu kamar ‘yan ƙungiya ɗaya, amma dai su ma da nasu tsarin shugabancin.

Ita kanta fassarar finafinan Indiya ana ganin ta taimaka wajen rage kallon finafinai na batsa da nuna tsiraici. Ko kun fahimce hakan?

Wannan gaskiya ne mun san da wannan, saboda ai ka san duk abin da mutum zai kalla kuma yana jin abin da ake cewa, to zai ga ma’anar abin da ake nunawa kuma zai ji abin da aka ce. kuma Alhamdulillah muna ƙoƙarin tace finafinai da za mu fassara. Sannan Hukumar tace finafinai ta Jihar kano ta taimaka mana wajen saka mu a cikin tsari na yadda za mu gudanar da sana’ar tamu domin kaucewa abin da ya saɓa wa al’adar mu da addinin mu.

Ita wannan ƙungiyar ta tsaya ne iya fassarar finafinan Indiya ko dai kuna samar da finafinai na Hausa?

E haka ne, a cikin mu akwai masu shirya finafinai, kamar Sultan Abdurrazaƙ da wasu ma da yawa a cikin ƙungiyar. Domin ko a kwanakin baya mun je wata ganawa da Shugaban Hukumar tace finafinai ta Jihar kano ya nuna jin daɗin sa da ya ga mutanen mu ba iya fassarar finafinan Indiya suka tsaya ba, suna yin finafinai na kasa, don yanzu ko fim aka kai masa na ‘yan wannan ƙungiya ya kan saurare mu ya bamu kulawar da ta kamata, don yana ƙarfafa mana saboda mu samu ci gaba. Kuma Alhamdulillah muna samun ci gaba ta wannan ɓangaren.

Da yake ka shigo da maganar alaƙar ku da gwamnati. Akwai ɓangaren masu fim ɗin Kannywood da ake ba su horo da kuma tallafin gudanar da sana’arsu, ko a ɓangaren ku kun samu wannan tallafin?

To gaskiya ba mu ci wannan gajiyar tallafin da gwamnati take bayarwa ba, kuma abin yana sosa wa mutanen mu rai. Suna ganin kamar an ajiye su a gefe ɗaya. Duk da mu ma muna cikin masu biyayya ga gwamnati kuma muna samar mata da kuɗaɗen shiga, don haka muke ganin kamar an ajiye mu a gefe ba a yi da mu. Amma dai ni a matsayina na shugaban ƙungiya na je na samu Abba El-Mustapha. kuma muna sa ran a shigar da mu nan gaba domin muma muna buƙatar tallafin.

To a yanzu da gwamnati za ta tallafa muku da me kike son ta tallafawar?

E to akwai abubuwa masu yawa, amma a irin wannan harkar tamu, abu na farko da muke son gwamnati ta tallafa mana shi ne jari, domin idan kana da jari, duk abin da ka tashi gabatar da shi, to za ka gabatar da shi ne cikin sauki. Domin a yanzu mutanen mu suna shan wahala saboda babu jari sosai a hannun su, saboda yanayin yadda kasuwancin yake buƙatar jari mai karfi, sai ya zama harkar duk muna kame-kame ne. 

Don haka muna kra ga Gwamna Abba kabir Yusuf na Jihar kano da ya tallafa wa masu sana’ar fassarar finafinan Indiya da kasuwancin su, don gaskiya muna buƙatar tallafin gwamnati a wannan harkar. 

Kai ba Gwamnatin Jihar kano ba har Gwamnatin tarayya muna neman taimakon ta a matsayin mu na ‘yan ƙasa da suke gudanar da harkokin kasuwanci bisa dokar ƙasa da kuma samar da aikin yi ga matasa sama da miliyan biyu, don haka muna ƙara kira ya kamata a dubi wannan ƙungiya a tallafa mata domin samar da ɗorewar kasuwancin.

To madalla mun gode.

Ni ma nagode sosai.

By ukarofi