Mazauna Abuja sun buƙaci gwamnati ta kafa ƙarfafan dokokin haya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Matsalar gidaje a Babban Birnin Tarayya, Abuja, na ci gaba da ta’azzara sakamakon tsadar haya, ƙarancin gidaje masu araha da kuma saurin ƙaruwa da yawan jama’a.

Lamarin ya sa samun ingantaccen masauki ya zama wani babban ƙalubale ga mazauna birnin, musamman ma’aikatan gwamnati, masu ƙaramin ƙarfi da kuma masu matsakaitan kuɗaɗen shiga.

Binciken da jaridar Blueprint ta gudanar ya nuna cewa ma’aikatan gwamnati, masu ƙananan sana’o’i da sauran masu ƙaramin albashi na daga cikin waɗanda wannan matsala ta fi shafa, yayin da masu gidaje ke ci gaba da ƙara kuɗin haya ba tare da wata doka da ke taƙaita hakan ba.

A cikin shekaru kusan 20 da suka gabata, yawan jama’ar Abuja ya ƙaru matuƙa, lamarin da ya tilasta wa dubban iyalai ƙaura zuwa yankunan da ke wajen tsakiyar birnin kamar Kubwa, Lugbe, Karu, Nyanya, Gwagwalada, Suleja a Jihar Neja, da kuma Mararaba, Masaka har ma da Keffi a Jihar Nasarawa domin samun gidajen da za su iya biya.

A kullum kafin fitowar alfijir, dubban ma’aikata kan taso daga waɗannan garuruwa zuwa wuraren aikinsu a cikin Abuja. Wasu na shafe sa’o’i biyu zuwa uku a hanya saboda rashin ikon biyan kuɗin haya a cikin birnin.

Masana harkokin gidaje sun danganta wannan matsala da hauhawar farashin kayayyaki, ƙaruwa da yawan jama’a, tsadar filaye, tashin farashin kayan gini, ƙarancin tsarin lamunin gidaje (mortgage), da kuma ƙarancin gidaje da ake buƙata a ƙasar. Wasu mazauna kuma sun zargi masu gidaje da nuna kwaɗayi wajen ƙara kuɗin haya ba tare da la’akari da halin tattalin arzikin jama’a ba.

Binciken ya kuma nuna cewa har ma masu zama a tsofaffin gine-ginen da suka wuce shekaru 20 ba su tsira daga matsalar ba. Duk da cewa yawancin gine-ginen ba a gyara su yadda ya kamata ba, masu haya ne ke ɗaukar nauyin gyare-gyaren, sannan daga baya a ƙara musu kuɗin haya ba tare da an mayar musu da kuɗin gyaran da suka kashe ba.

Haka kuma, matsalar ta haddasa cunkoson jama’a a wasu unguwanni, ƙarin cunkoson ababen hawa, tashin kuɗin sufuri da kuma yaɗuwar matsugunan da ba su da tsari, abin da ke ƙara wa kayayyakin more rayuwa da ayyukan gwamnati nauyi.

Dillalan gidaje da sauran masu ruwa da tsaki ta nuna cewa kuɗin haya na ƙaruwa cikin sauri, yayin da masu gidaje ke buƙatar a biya haya ta shekara ɗaya ko biyu gaba ɗaya, tare da kuɗin dillanci, kuɗin lauya da kuma kuɗin kariya (caution fee).

Wata mazauniyar Abuja, Esther Onwuzulike, ta ce tsadar haya ta zarce ƙarfin mafi yawan mazauna, har ma da waɗanda ke wajen tsakiyar birnin. Ta bayyana cewa a baya tana zaune ne a Garki, amma ta koma Karu saboda tsadar haya. Ta ce kuɗin hayar ɗakin kwana ɗaya da take zaune tare da iyalanta ya tashi daga naira 700,000 zuwa Naira miliyan 1.2.

“Har yanzu ina roƙon mai gidan ya amince na biya a kashi biyu, domin duk ƙoƙarin da na yi na neman gida mai rahusa ya ci tura. Na kai har Orozo, amma babu ruwa, babu hanyoyi masu kyau, sannan matsalar tsaro ta yi yawa. Don haka ba ni da zaɓin barin gidan yanzu,” inji ta.

Ta yabawa gwamnatin da ake ciki kan ayyukan more rayuwa da ake yi, amma ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta Babban Birnin Tarayya su mayar da hankali wajen samar da gidaje masu araha ga talakawa.

Wani mazaunin Kubwa, Abubakar Habila, ya dora alhakin tashin kuɗin haya kan dillalan gidaje, yana mai cewa su ne ke ƙarfafa masu gidaje su ƙara kuɗin haya domin su sami ƙarin kaso.

Ya ce sau biyu an kore shi daga gidan haya cikin shekaru huɗu da suka gabata, kuma yana fargabar sake fuskantar hakan idan hayarsa ta cika a shekara mai zuwa.

Habila ya zargi masu gidaje a Abuja da haɗa kai wajen tilasta wa masu haya su amince da ƙarin kuɗin haya da ya kai kashi 100 cikin ɗari ko kuma su fice, domin sababbin masu haya sun fi shirye-shiryen biyan sabon farashin tare da kuɗin dillanci da na lauya da ba sa sassauci.

Sai dai wani dillalin gidaje mai suna Ahmeed ya ce hauhawar farashin kayayyaki ce ke haddasa ƙarin haya, ba wai dillalai ba.

Dokokin Nijeriya sun tsara yadda ake hulɗa tsakanin mai gida da mai haya, musamman kan korar mai haya.

A Babban Birnin Tarayya kuwa, Dokar Karbo Gidaje (Recoɓery of Premises Act) ce ke tafiyar da irin waɗannan al’amura. Sai dai babu wata doka da ta kayyade adadin kaso na ƙarin kuɗin haya da mai gida zai iya yi. Wannan ne ya sa masu haya ke kira da a samar da dokar da za ta hana ƙarin haya ba gaira ba dalili. Habila ya ce akwai buƙatar samar da doka da za ta kare masu haya daga ƙarin kuɗin haya cikin gaggawa.

Ya ce, “Na biya naira miliyan biyu a matsayin haya, na biya naira dubu 200 kuɗin dillanci da wasu naira dubu 200 kuɗin lauya. Bayan shekara biyu kuma ana son a ninka min kuɗin haya. Daga ina zan samo wannan kuɗi? Shin ba wannan ne ke ƙarfafa cin hanci ba?”

Duk da matsalar ƙarancin gidaje, binciken Blueprint ya gano cewa akwai gidaje da dama da aka kammala a manyan unguwannin Abuja amma babu masu zama a cikinsu tsawon watanni ko shekaru.

Masana sun danganta hakan da yadda wasu ke sayen gidaje domin adana dukiya kawai ba wai don a zauna a cikinsu ba.

Wata tsohuwar ma’aikaciyar Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA), Beatrice Ajuma, ta ce gwamnati na da bayanan duk masu filaye da gidaje a Abuja, don haka ya dace ta gudanar da cikakken bincike domin gano masu waɗannan gidaje da ba a amfani da su.

Ta ce hakan zai taimaka wajen sanin ko matsalar ƙarancin gidaje ce ko kuma rashin amfani da gidajen da ake da su.

Bincike ya nuna cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin rage gibin gidaje ta hanyar shirye-shiryen Renewed Hope Cities and Estates, Shirin Gidajen Jama’a (NSHP Social Housing Initiatiɓe), sauƙaƙa tsarin mallakar filaye da kuma samar da lamunin gidaje ta Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya (FMBN).

Sai dai wasu mazauna sun ce samun damar shiga waɗannan shirye-shiryen na da wahala. Misis Chinasa Chukwudi ta ce ta yi rajista a shirin gidajen gwamnatin tarayya, ta biya kuɗin neman gida na naira 10,000, amma daga baya aka sanar da ita cewa ba ta cancanta ba duk da tana samun albashin naira 250,000 a wata. Ta ce, hakan ya sa take tambayar ko gidajen na gwamnati an ware su ne kawai domin manyan mutane da ma’aikatan gwamnati.

Wani mazaunin Abuja da shi ma aka ƙi amincewa da buƙatarsa ya buƙaci gwamnati ta bayyana ƙa’idojin cancanta dalla-dalla tun kafin mutane su fara rajista.

Masana sun ba da shawarar faɗaɗa tsarin lamunin gidaje, sauƙaƙa tsarin mallakar filaye, inganta hanyoyi da ababen more rayuwa a garuruwan da ke kewaye da Abuja, ƙarfafa haɗa gidaje masu araha da masu tsada a wurare guda, da kuma sake duba manufofin da ke ƙarfafa sayen gidaje domin kasuwanci maimakon zama.

Haka kuma sun buƙaci Gwamnatin Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta hanzarta aiwatar da shirye-shiryen samar da gidaje masu araha, ta sauƙaƙa samun lamunin gidaje, ta sake duba tsarin rabon filaye, tare da bai wa masu zuba jari a fannin gidaje tallafin da zai rage tsadar gine-gine.

By ukarofi

Leave a Reply