Ai ba a sake rubuta tarihi – Martanin Atiku ga Obasanjo kan nadamar shugabancinsu tare

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar ya yi martani da babbar murya ga tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo kan kalamansa na kwanan nan, yana mai bayyana su a matsayin wata rashin nasara ta yunƙurin sake rubuta tarihi.

Ya ce, babu wata buƙata ta raɗin kai da za ta iya goge raɗaɗin matsayarsa ta ƙin amincewa ajandar samar da tsarin wa’adi na uku ko wata rawa da ya taka a harkar siyasar Obasanjo.

Martanin Atikun ya biyo bayan sukar Obasanjo ne akansa yayin wata hira, yana mai cewa tarihi ne zai yi alaƙanci a tsakaninsu bisa hujjojin gaskiya ba ƙawa-zucin wani ba.

A sanarwar da Mai taimaka wa Atiku kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu ya fitar, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kalli hirar da aka yi da Obasanjo cikin ƙunci a madadin fushi, inda ya ƙara da cewa kalaman nasa sun fi karkata ga wanda ke ƙoƙarin neman a sauya tarihi don buƙatar kansa.

A cewar Atiku, rikicin da ke tsakaninsa da Obasanjo abu ne sananne ga ‘yan Nijeriya.

Ya bayyana cewa, batun neman wa’adi na uku a Obasanjo ya yi da kuma nuna adawarsa akan haka ba don maslahar kai ba n, saidai mataki ne da ya ɗauka domin bayar da kariya ga dimukraɗiyyar Nijeriya don goben al’umma.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma ce akwai takaici a ce wanda aka ƙi ba wa goyon bayan ida manufarsa ta saɓa wa doka ya kuma koma yana zargin waɗanda suka bai wa dokar kariya.

By Babaji

Leave a Reply