Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Aƙalla ‘yan Nijeriya miliyan 16.99 ake hasashen za su fuskanci matsananciyar yunwa nan da watan Janairun 2027, a cewar sabon rahoton Cibiyar Kula da Gargaɗin Matsalar Yunwa (FEWS NET), wanda ya nuna cewa matsalar ƙarancin abinci a ƙasar na ci gaba da tsananta duk da ana sa ran girbin damina zai ɗan rage ta.
Rahoton na cikin Takaitaccen Hasashen Tallafin Abinci na watan Yulin 2026 da FEWS NET ta fitar, wanda ya yi nazari kan yadda matsalar yunwa ke ƙara ta’azzara a ƙasashen da rikice-rikice da sauyin yanayi suka fi shafa, ciki har da Nijeriya.
FEWS NET, wata cibiyar gargaɗin yunwa da Gwamnatin Amurka ke tallafawa, ta yi hasashen cewa adadin mutanen da za su buƙaci agajin gaggawa na abinci a Nijeriya zai ragu zuwa tsakanin miliyan 16 da miliyan 16.99 nan da Janairun 2027, idan aka kwatanta da tsakanin miliyan 20 zuwa miliyan 20.99 da aka kiyasta a watan Yulin 2026.
Sai dai duk da wannan raguwar da ake tsammani, rahoton ya nuna cewa adadin ya fi na watan Janairun shekarar da ta gabata, sannan ya zarce matsakaicin adadin da aka samu cikin shekaru biyar da suka gabata, lamarin da ke nuna cewa matsalar yunwa a Nijeriya na ƙara muni.
Rahoton ya sanya Nijeriya a matsayi na huɗu cikin ƙasashen da ke da mafi yawan mutanen da ke fama da matsananciyar yunwa, bayan Sudan, Pakistan da Jamhuriyar Dimokuraciyyar Kongo (DRC), yayin da ta fi ƙasashe irin su Yemen da Afghanistan.
Har ila yau, Nijeriya na cikin ƙasashe huɗu kacal da ake sa ran kowacce za ta bayar da sama da kashi 10 cikin 100 na mutane miliyan 145 zuwa miliyan 155 da ake hasashen za su buƙaci agajin gaggawa na abinci a cikin ƙasashe 30 da FEWS NET ke sa ido a kansu nan da Janairun 2027.
A cewar rahoton, rikice-rikicen tsaro, rushewar hanyoyin samun abin masarufi, hana manoma shiga gonakinsu da kuma raguwar kuɗaɗen shiga na iyalai, musamman a Arewacin Nijeriya, su ne manyan abubuwan da ke ƙara haddasa matsalar yunwa.
Ko da yake ana sa ran girbin damina da zai kammala a watan Disamba zai ɗan rage matsalar, FEWS NET ta gargaɗi cewa wannan sauƙin ba zai wadatar ba saboda iyalai da dama da rikici ya shafa har yanzu ba sa iya komawa gonakinsu.
Rahoton ya ce duk da girbin da ake tsammani, farashin kayan abinci zai ci gaba da kasancewa mai tsada sakamakon raguwar amfanin gona da matsalolin samar da kayayyaki, tare da dogaron da iyalan da rikici ya shafa ke yi da kasuwanni wajen samun abinci.
Rahoton ya bayyana cewa al’ummomin da rikici ya fi shafa a Arewa maso Gabas, musamman waɗanda rikici ya killace tare da hana zirga-zirga, za su ci gaba da kasancewa a matakin “Gaggawa” na yunwa.
A tsarin Rarrabe Matsayin Tsaron Abinci na Duniya (Integrated Food Security Phase Classification – IPC), wannan mataki shi ne na huɗu cikin matakai biyar, kuma yana gab da matakin bala’in yunwa (Famine).
Matakin “Gaggawa” na nufin iyalai na fama da matsanancin ƙarancin abinci, ƙaruwar rashin abinci mai gina jiki da mace-mace, ko kuma suna rayuwa ne ta hanyar sayar da muhimman kadarorinsu kamar filayen noma da dabbobi.
Bisa ga bayanan rahoton, adadin mutane miliyan 16 zuwa miliyan 16.99 da ake hasashen za su fuskanci yunwa a Janairun 2027 ya kai tsakanin kashi biyar zuwa 10 cikin 100 na yawan al’ummar Nijeriya.
Ko da yake wannan ya yi ƙasa da hasashen watan Yulin 2026 na mutane miliyan 20, FEWS NET ta ce idan aka kwatanta da shekarun baya, matsalar yunwar na ci gaba da ƙaruwa.
Ta bayyana rikici, matsin tattalin arziki da sauyin yanayi a matsayin manyan abubuwan da ke haddasa matsalar, irin waɗanda ke addabar ƙasashe kamar Sudan da Pakistan.
Rahoton ya nuna cewa a halin yanzu Nijeriya ce ta biyu a duniya wajen yawan mutanen da ke buƙatar tallafin abinci, bayan Sudan.
Sai dai ana sa ran nan da Janairun 2027 Pakistan za ta zarce Nijeriya, inda ake hasashen adadin masu fama da yunwa a can zai tashi daga kusan miliyan 12 zuwa miliyan 17.99, wanda zai sa Nijeriya ta koma matsayi na huɗu.
FEWS NET ta kuma yi gargaɗin cewa ƙasashe biyar na daf da shiga matakin bala’in yunwa, wanda shi ne mafi muni a ma’aunin yunwa, kuma ke tattare da matsanancin ƙarancin abinci, yunwa mai tsanani da mace-mace sakamakon rashin abinci mai gina jiki.
ƙasashen sun haɗa da Sudan, Sudan ta Kudu, Somalia, Mali da kuma Chadi, wadda ke karɓar ‘yan gudun hijirar da suka tsere daga rikicin Sudan.
Cibiyar ta ce hasashenta ya haɗa da mutanen da ke cikin matakin IPC Phase 3 ko sama da haka, da kuma waɗanda za su shiga wannan mataki idan ba a ci gaba da kai musu agajin jin ƙai ba.
Ta kuma bayyana cewa, sabanin wasu ƙasashe da ake amfani da sa ido daga nesa wajen tattara bayanai, hasashen da aka yi wa Nijeriya ya samo asali ne daga bincike da sa ido kai tsaye a cikin ƙasar.
