Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da rajistar ADC da wasu jam’iyyu huɗu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta soke hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) ta cire rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) da wasu jam’iyyun siyasa huɗu.

A hukuncin da alkalai uku suka yanke baki ɗaya, kotun ta bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron shari’ar, saboda ƙarar da aka shigar ba ta cika ka’idojin doka ba. Haka kuma ta ce babu ingantacciyar hujja da za ta ba da damar cire rajistar jam’iyyun.

Kotun ta kuma bayyana cewa alkalin Babbar Kotun Tarayya ya yi watsi da hujjojin da ke nuna cewa jam’iyyun sun taɓa lashe kujeru a zaɓukan da suka gabata, duk da cewa akwai umarnin dakatar da ci gaba da sauraron shari’ar da Kotun ɗaukaka ƙara ta bayar.

Sakamakon haka, kotun ta tabbatar da cewa jam’iyyun da abin ya shafa har yanzu suna da cikakkiyar rajista kuma suna da damar shiga harkokin zaɓe.

Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da ADC, Action Peoples Party (APP), Action Alliance (AA), Accord Party (AP) da Zenith Labour Party (ZLP).

Tun da farko, Babbar Kotun Tarayya ta umarci INEC da ta cire rajistar jam’iyyun biyar tare da hana su shiga zaɓen 2027, bayan wata ƙungiya mai suna National Forum of Former Legislators (NFFL) ta yi zargin cewa sun gaza cika wasu sharuddan kundin tsarin mulki. Sai dai jam’iyyun da INEC sun ɗaukaka ƙara, lamarin da ya kai ga soke hukuncin da kuma tabbatar da ci gaba da rajistarsu.

By ukarofi