Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa alƙawarin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, na yin wa’adi ɗaya kacal idan ya lashe zaɓen 2027, ba zai amfani muradun siyasar yankin Kudu maso Gabas ba.
Mai taimaka wa Mataimakin Shugaban ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Sadarwa, Stanley Nkwocha, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan kalaman Obi a wata hira da ya yi da Channels Teleɓision, inda ya ce a shirye yake ya yi wa’adin shekara huɗu kawai.
Nkwocha ya ce burin al’ummar Ndigbo na samar da shugaban ƙasa ya fi muradin mutum ɗaya girma, yana mai cewa ya kamata a gina shi bisa haɗin kai, tattaunawa da kuma amincewar sauran yankunan ƙasar.
Ya kuma ce idan rahotannin da ke cewa Rabiu Musa Kwankwaso zai zama mataimakin Obi tare da yarjejeniyar cewa zai gaje shi a shekarar 2031 gaskiya ne, hakan ba zai amfani yankin Kudu maso Gabas ba.
A cewarsa, Obi bai samu isasshen goyon baya daga Arewa da Kudu maso Yamma a zaɓen 2023 ba, yana mai cewa ko da ya ƙulla ƙawance da Kwankwaso, hakan kaɗai ba zai tabbatar masa da nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Nkwocha ya ƙara da cewa zai fi dacewa Peter Obi ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu damar kammala wa’adinsa na shekaru takwas, sannan ya haɗa kai da shugabannin Kudu maso Gabas domin gina tubalin neman shugabancin ƙasa a nan gaba.
