Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ba shi da wani laifi da zai hana a karɓe shi bayan ya koma cikin tafiyar siyasar da ta tsayar da shi takara.
Wike ya yi wannan bayani ne ranar Talata bayan duba ayyukan tituna da ake gudanarwa a Abuja, inda ya ce “babu zunubi a siyasa,” yana mai cewa dawowar Fubara mataki ne da ya dace kuma zai ƙarfafa haɗin kai a jam’iyyar.
Ya ce komawar gwamnan cikin tafiyar siyasar ta su zai taimaka wajen bunƙasa ci gaban Jihar Ribas tare da ƙarfafa shirin sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Ministan ya bayyana cewa tun da farko ya yi hasashen Fubara zai dawo cikin tafiyar siyasar da ta samar da shi, yana mai ƙara da cewa an karɓe shi hannu bibbiyu domin su ci gaba da aiki tare.
A makon da ya gabata ne Fubara ya sanar da komawarsa sansanin siyasar Wike, inda ya bayyana goyon bayansa ga Rainbow Coalition tare da nuna goyon baya ga takarar Shugaba Tinubu a wa’adi na biyu. Haka kuma ya buƙaci magoya bayansa su mara wa ‘yan takarar ƙungiyar baya a zaɓe mai zuwa.
Wike ya kuma yaba da ci gaban ayyukan titunan ISEɗ Road Corridor da Apo–Karshi a Abuja, yana mai jaddada cewa gwamnatin FCT za ta ci gaba da kammala dukkan ayyukan raya ƙasa da ta gada maimakon yin watsi da su.
