Uba Sani ya zaɓi Jerry Adams a matsayin mataimakinsa, ya kawo ƙarshen tikitin Musulmi da Musulmi a Kaduna

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya zaɓi Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS), Jerry Adams, a matsayin ɗan takarar mataimakinsa a zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Gwamnan ya sanar da hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Talata, inda ya ce matakin ya nuna ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da adalci, haɗin kai da bai wa kowa dama ba tare da nuna bambanci ba.

Adams, wanda ƙwararren masani ne a harkar haraji da gudanar da mulki, zai maye gurbin Mataimakiyar Gwamna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe, wadda ba za ta kasance a tikitin APC ba a zaɓen 2027.

Hakan ya kawo ƙarshen tsarin tikitin Musulmi da Musulmi da tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, ya gabatar a zaɓen 2023 lokacin da ya tsayar da Uba Sani da Dakta Hadiza Balarabe a matsayin ‘yan takarar APC.

“Wannan mataki yana nuna manufar haɗin kai”

A cikin sanarwar tasa, Gwamna Uba Sani ya ce zaɓin Jerry Adams ya wuce zaɓen mataimakin gwamna kawai.

Ya ce matakin ya sake tabbatar da manufofin gwamnatinsa na adalci, daidaito, haɗa kan al’umma da kuma tabbatar da cewa kowane ɗan jihar Kaduna yana jin yana da muhimmanci a cikin gwamnati.

Gwamnan ya bayyana cewa bambancin addinai da ƙabilun da ke Kaduna wata babbar ni’ima ce, ba matsala ba.

Ya ce gwamnatinsa ta tabbatar da cewa ayyukan raya ƙasa kamar gina hanyoyi, makarantu, asibitoci, samar da ruwa, bunƙasa noma da shirye-shiryen tallafa wa al’umma sun isa dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar ba tare da nuna son kai ba.

Ya kuma ce haɗin gwiwar da gwamnatinsa ta yi da sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da ƙungiyoyin al’umma ya taimaka wajen inganta zaman lafiya da tsaro a jihar.

Gwamna Uba Sani ya bayyana Jerry Adams a matsayin gogaggen ma’aikacin gwamnati kuma ƙwararren mai gudanarwa wanda ya sauya fasalin Hukumar Tara Haraji ta Kaduna ta zama ɗaya daga cikin hukumomin tara haraji mafi nagarta a Nijeriya.

Ya ce Adams ya taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga na cikin gida ta hanyar gaskiya, ƙwarewa da sabbin tsare-tsare, lamarin da ya ba gwamnati damar ƙara zuba jari a fannonin ilimi, lafiya, noma da ababen more rayuwa.

Ya kuma ce Adams mutum ne mai gaskiya, tawali’u da kishin haɗin kan al’umma.

Sanarwar ta zo ne bayan ɗan takarar gwamna na jam’iyyar ADC, Isah Ashiru, ya bayyana Dakta John Ayuba Kantiyok a matsayin mataimakinsa domin zaɓen 2027.

Da wannan, manyan jam’iyyun biyu sun kammala zaɓen ‘yan takarar mataimakan gwamna, abin da ke nuna cewa siyasar jihar Kaduna za ta ƙara ɗaukar zafi yayin da ake tunkarar zaɓen 2027.

Zaɓen wanda zai yi wa Gwamna Uba Sani mataimaki ya jawo ce-ce-ku-ce a siyasar Kaduna, domin mutane da dama na son sanin ko zai ci gaba da tsarin tikitin Musulmi da Musulmi da aka yi amfani da shi a zaɓen 2023, ko kuwa zai koma tsarin Musulmi da Kirista.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Nijeriya da suka fi yawan bambancin addinai da ƙabilu, kuma batun daidaito da wakilci na ci gaba da kasancewa muhimmin batu a siyasar jihar.

Da zaɓen Jerry Adams, Gwamna Uba Sani ya mayar da tikitin APC zuwa tsarin Musulmi da Kirista, matakin da ake sa ran zai kasance ɗaya daga cikin manyan batutuwan siyasa kafin zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.

By ukarofi

Leave a Reply