Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
ƙungiyar Masu Sarrafa Kwakwan Manja ta ƙasa (NPPAN), ta bayyana cewa Nijeriya na da burin kaiwa ga cikakkiyar wadatar manja tare da samun gagarumar kason kasuwar duniya nan da shekarar 2050.
Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alphonsus Inyang, ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NANS) a gefen taron tantance Tsarin Bunƙasa Noman Kwakwan Manja na ƙasa da aka gudanar a Abuja.
Ya ce wannan buri zai tabbata ne ta hanyar aiwatar da Tsarin Bunƙasa Noman Kwakwan Manja na ƙasa yadda ya kamata, wanda zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin da ƙasar ke samarwa.
A cewarsa, a halin yanzu Nijeriya na samar da tsakanin ton miliyan 1.4 zuwa 1.5 na manja a shekara, amma ana sa ran wannan zai tashi zuwa tsakanin ton miliyan 9 zuwa 10 nan da shekarar 2050.
Inyang, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban Kwamitin Fasaha na tsara wannan shiri, ya jaddada cewa za a cimma wannan nasara ne ta hanyar ƙarfafa kananan manoma domin su ƙara yawan amfaninsu.
Ya ƙara da cewa shirin zai kuma faɗaɗa noman kwakwan zuwa wasu jihohi kamar Taraba, Neja da kuma Kogi, domin inganta samarwa a faɗin ƙasar.
A cewarsa, jihar Taraba na da filin noma mai faɗi da ya kai kilomita murabba’i 69,000, wanda ya zarce damar da yawancin jihohin Kudancin Nijeriya ke da ita wajen noman kwakwan. Haka kuma, yana da isasshen hasken rana da ruwa a wasu yankuna, wanda zai taimaka wajen bunƙasa wannan noma.
Ya bayyana cewa wannan sabon tsari zai mayar da Nijeriya babbar ƙasa mai tasiri a harkar manja a duniya.
A cikin tsarin, za a kafa Majalisar Noman Kwakwan Manja ta ƙasa (NOPC), tare da Asusun Bunƙasa Noman Kwakwan Manja da kuma Asusun Tallafa wa ƙananan Manoma.
Haka kuma, cibiyar bincike ta Kwakwan Manja za a sauya ta zuwa Hukumar Kwakwan Manja ta Nijeriya domin kula da bincike, bunƙasa fasaha da ƙirƙire-ƙirƙire a wannan fanni.
Sai dai Inyang ya nuna damuwa kan matsayin Nijeriya a duniya, inda aka sanya ta a matsayi na biyar wajen samar da manja, duk da cewa ita ce ta farko a Afirka wajen samarwa, amfani, shigo da kuma fitar da wannan kaya.
Ya danganta koma bayan da aka samu a wannan fanni da rashin ingantaccen tsari da tsarin shugabanci, wanda ya haifar da rashin tsari mai kyau ga masu zuba jari.
A cewarsa, sabon tsarin zai kawo ingantaccen tsarin shugabanci irin wanda ake amfani da shi a ƙasashe irin su Malaysia da Indonesia, waɗanda su ne kan gaba a duniya wajen samar da manja.
Ya ƙara da cewa gwamnati ta samar da yanayi mai kyau domin bunƙasa wannan fanni, tare da ƙarfafa ’yan kasuwa da masu zuba jari su yi anfani da sabbin manufofin.
A nasa ɓangaren, babban mai ba da shawara a kamfanin Foremost Deɓelopment Serɓices, Fatai Afolabi, ya ce manufar shirin ita ce gina tsarin noman kwakwan manja mai ɗorewa, wanda zai tabbatar da wadatar ƙasa, gasa a kasuwa, da kuma haɗa kowa cikin samarwa.
Ya bayyana cewa za a yi amfani da tsarin haɗaka tsakanin manyan gonaki da kananan manoma, tare da amfani da hanyoyin zamani, bincike da kuma ingantaccen tsarin kasuwanci.
