’Yan sanda a Katsina sun daƙile harin ‘yan bindiga tare da ƙwato bindiga da babur

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina ta daƙile wani hari da ‘yan bindiga suka kai a ƙauyen Sabon Gulbi da ke Ƙaramar hukumar Musawa, inda ta ƙwato bindigar AK-47, harsasai da babur.

Wata sanarwa da Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya fitar, lamarin ya faru ne bayan da rundunar ’yan sanda daga ofishin Musawa ta samu kiran gaggawa cewa wasu masu ɗauke da makamai sun shiga ƙauyen.

Bayan samun bayanin, DPO na ofishin Musawa ya jagoranci tawagar haɗin gwiwa da ta ƙunshi jami’an ’yan sanda da na rundunar tsaron al’umma ta Jihar Katsina (KSCWC) zuwa yankin.

Jami’an tsaron sun isa wurin cikin gaggawa inda a kai ta ɗauki ba dadi kafin samun nasarar fatattakar ‘yan bindigan,”Inji DSP Abubakar Sadiq.

Rundunar ‘yan sandan ta sanar da kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigan yayin artabun, yayin da wasu suka tsere daga yankin.

Bayan gudanar da bincike a wurin, jami’an tsaro sun ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya, mujalla mai harsasai guda biyar da kuma babur.

A cewar DSP Abubakar Sadiq, jami’an tsaro za su cigaba da farautar sauran yan bindigan da suka tsere domin.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar Katsina, CP Ali Umar Fage, ya yaba wa jami’an tsaro bisa jajircewa, ƙwarewa da haɗin kan da suka nuna. Ya kuma yaba da bayanan gaggawa da suka taimaka wajen kai martani cikin lokaci. Ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙarin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da buƙatar jama’a su kasance masu lura da abubuwan da ke faruwa a kewaye da su, su kuma gaggauta kai rahoton duk wani abu da ya tayar musu da hankali ga ofishin ’yan sanda ko hukumar tsaro mafi kusa.

By ukarofi