Matsalar tsaro, ambaliya da rashin kyan hanyoyi ke haddasa tsadar abinci — AFAN

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Manoma ta ƙasa (AFAN) ta bayyana cewa duk da matakan da Gwamnatin Tarayya ke ɗauka domin bunƙasa noma da rage hauhawar farashin kayan abinci, matsalolin rashin tsaro, ambaliyar ruwa da kuma lalacewar hanyoyin karkara na ci gaba da kawo cikas ga samar da abinci a faɗin ƙasar.

Babban Sakataren AFAN na ƙasa, Femi Oke, ne ya bayyana hakan yayin da yake mayar da martani kan sabon rahoton Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) game da hauhawar farashin kayayyaki na watan Yuni.

Ya ce, duk da cewa an samu ɗan sauƙi a hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya, farashin kayan abinci ya ci gaba da ƙaruwa saboda matsalolin da manoma ke fuskanta. 

A cewarsa, rashin tsaro a yankunan da ake noma manyan amfanin gona ya sa manoma da dama ba sa iya komawa gonakinsu saboda tsoron hare-haren ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane.

Ya ce, duk ƙoƙarin da gwamnati ke yi na samar da yanayi mai kyau ga noma ba zai haifar da sakamakon da ake buƙata ba matuƙar manoma ba su samu cikakken tsaro ba.

Femi Oke ya kuma danganta tashin farashin kayan abinci da mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa da suka lalata gonaki a wasu sassan ƙasar, lamarin da ya rage yawan amfanin gona da ke shiga kasuwanni.

Ya ce hakan ya ƙara jefa tsarin samar da abinci cikin mawuyacin hali. 

Baya ga matsalar tsaro da ambaliya, AFAN ta nuna cewa lalacewar hanyoyin karkara na ƙara jefa manoma cikin asara.

A cewarsa, hanyoyin da ba su da kyau suna hana sauƙin jigilar amfanin gona daga gonaki zuwa kasuwanni, wanda hakan ke ƙara kuɗin sufuri da kuma tsadar kayan abinci ga masu saye.

Ya yi nuni da cewa jihohi da dama ba su aiwatar da Shirin Hanyoyin Karkara da Kasuwancin Noma (RAAMP) yadda ya kamata ba, duk da irin muhimmancin da shirin ke da shi wajen haɗa yankunan noma da manyan kasuwanni. Ya ce idan ba a gyara waɗannan hanyoyi ba, farashin kayan abinci zai ci gaba da tashi saboda masu sufuri suna ɗora wa masu amfani ƙarin kuɗin jigila. 

AFAN ta buƙaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi su ƙara haɗin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu wajen inganta harkokin sufuri da kasuwancin noma. ƙungiyar ta ba da shawarar a samar wa kowace jiha motocin jigilar kayan gona domin rage asarar amfanin gona da kuma sauƙaƙa kai shi kasuwa cikin lokaci.

A cewar Femi Oke, samar da irin waɗannan motocin zai taimaka wajen rage kuɗin jigila, wanda hakan zai sauƙaƙa farashin kayan abinci ga al’umma.

Sai dai ya yabawa Gwamnatin Tarayya kan wasu matakan tallafin da take bai wa manoma.

Ya ce kwanan nan gwamnati ta raba takin zamani kyauta a jihohi 26 da Babban Birnin Tarayya Abuja, inda sama da manoma 12,000 suka amfana da shirin.

Ya bayyana wannan a matsayin wani mataki mai kyau da zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona idan aka haɗa shi da ingantaccen tsaro da kyawawan hanyoyin karkara. 

ƙungiyar ta jaddada cewa rage tsadar kayan abinci ba zai yiwu ta hanyar manufofin kuɗi kaɗai ba, sai an magance matsalolin da ke hana manoma noma cikin kwanciyar hankali. Ta ce ƙarfafa tsaro, hana ambaliya, gyaran hanyoyin karkara da kuma ci gaba da tallafa wa manoma su ne manyan hanyoyin da za su tabbatar da wadatar abinci da rage tsadar rayuwa a Nijeriya.

AFAN ta kuma yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki su haɗa kai domin kare manoma da bunƙasa harkar noma, tana mai cewa noma ne ginshiƙin samar da wadataccen abinci da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa. 

By ukarofi

Leave a Reply