A shirye muke mu tattauna da gwamnati – Boko Haram ga iyalan mutane 50 da ta sace

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shigo tsakani domin a tattaunawa akan sako sama da mazaunan Jihar Borno 50 da aka yi garkuwa da su wajen sanya wani ɗan jarida a matsayin ɗan tsakani.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa ba ta manta da ɗaliban makarantar firamare da sakandare ta Askira-Uba da aka sace ba a ranar 15 ga watan Mayu, tana mai cewa dakarun tsaro na aiki tuƙuru wajen ganin an ceto su cikin ƙoshin lafiya.

An ruwaito cewa, 13 daga ciki sun haɗa da jaririyar wata bakwai da mahaifiyarta tare da ‘yarta mai shekara uku da kuma ma’aurata masu tafiya tare, waɗanda aka sace su a ranar 15 ga Afrilu a lokacin da suke tafiya daga Biu zuwa Maiduguri.

Sauran sun haɗa da wasu sababbin ɗaliban da suka kammala makarantar gaba da sakandare da wasu biyu ‘yan gida ɗaya da aka nemi su shiga bayan mota saboda ba su da kuɗin biyan sufuri.

A ranar Juma’a ne mai magana da yawun iyalan da aka sacen, Hassan Yati ya tabbatar da cewa masu garkuwar sun bayar da hujjojin hotuna da ɗaukar murya kan cewa mutanen suna raye.

A cewarsa, ‘yan ƙungiyar ta’addancin sun buƙaci gwamnati ta buɗe fagen tattaunawa ta hannun wani ɗan jarida da suka amince da shi a matsayin ɗan tsakani, saidai bai faɗi waye ɗan jaridar ba.

Ya kuma ce iyalan sun shirya bayar da dukkan bayanan da ake buƙata matuƙar gwamnati ta nuna tana da ra’ayin karɓar tayin tattaunawar.

A ranar 23 ga Yuli ne Cibiyar yaɗa labarai na Ƙungiyar ‘Yan jarida ta Ƙasa (NUJ) a Maiduguri ta karɓi baƙuncin iyalai da ‘yan uwan waɗanda aka sacen a lokacin da suka cika kwanaki 100 a tsare domin yin magiya ga gwamnati kan ta hoɓɓasa wajen ceto su.

Har yanzu dai ana fargabar halin da ɗalibai 78 ke ciki, waɗanda sace a wasu makarantu a mabambanta hare-hare a Ƙaramar hukumar Askira-Uba da ke Jihar Borno.

By Babaji