Ɗaukar ka a matsayin abokin tafiya shi ne babban kuskurena – Obasanjo ga Atiku

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya bayyana matakinsa na ɗaukar tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Atiku Abubakar a matsayin abokin tafiyarsa a zaɓen shugaban ƙasa na 1999 a matsayin mafi girman kuskure a shugabancinsa.

Obasanjo ya bayyana haka ne a ranar Juma’a a Legas, a lokacin da yake tattaunawa da daɗaɗɗen ɗan fafutuka, Charles Oputa da aka fi sani da Charly Boy, a wani taron Gidauniyar Charly Boy da aka shirya domin karrama Marigayi Chukwudifu Oputa.

Tsohon shugaban ƙasar, wanda ya jagoranci Nijeriya tare da Atiku a tsakanin 1999 da 2007, ya ce kowane shugaba na yin kuskure a lokacin da yake ofis, yana mai cewa zaɓar Atiku na daga cikin ababen da yake nadamarsu a tarihin siyasarsa.

A cewarsa, ba zai ɗauke shi ba matuƙar ya san zai gano wasu ababe akansa da ka iya hana shi ɗaukarsa a matsayin abokin tafiya a malkin nasa.

Obasanjo ya bayyana haka ne yayin Charly Boy ya tambaye shi akan ya faɗi mafi girman kuskuren da ya yi a matsayinsa na shugaban Nijeriya.

“Mutumin da na ɗauka a matsayin abokin tafiyata, na biyuna. Idan da na san shi kamar yadda na gano wane ne shi daga baya, da ba zan ɗauke shi ba,” inji Obasanjo.

Tsohon shugaban ya kuma tirje akan cewa ba shi da wata mummunar manufa ta raɗin kansa akan Turakin Adamawar duk da tsamin dangantakarsu a siyasa, saidai ya yi hakan ne saboda maslahar siyasarsa.

Da fari, tsofaffin jagororin sun yi mulki cikin zaman lafiya a wa’adinsu na farko, amma daga bisani an fara samun tsama ne a tsakaninsu a lokacin da Atiku ya ƙi amincewa da yunƙurin waɗanda suke na hannun daman Obasanjo ne akan a yi wa kundin tsarin mulkin Nijeriya kwaskwarima ta yadda zai ba wa tsohon shugaban ƙasar damar yin wa’adi na uku a kujerar mulkin Kasar.

By Babaji

Leave a Reply