Tinubu ne zai karɓi gawar Buhari a Katsina

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne zai tarbi gawar tsohon shugaba Muhammadu Buhari a Katsina, domin yi masa jana’iza a Daura.

Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ne ya tabbatar da hakan da yammacin yau Litinin a Abuja.

A cewar ministan, da misalin ƙarfe 12 na ranar yau Talata ake sa ran gawar marigayi tsohon shugaban za ta isa Katsina.

Sannan za a yiwa shugaban faretin ban girma a filin jirgin saman Katsina, kafin daga bisani a wuce garin Daura da gawarsa.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima yanzu haka na Landan, kuma shi ne zai rako gawar har Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Najeriya ta kafa kwamiti na musamman da za su tsara jana’izar da kuma duk wani abu da ake buƙata wajen binne tsohon shugaban.

By ukarofi