Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau
Gwamnatin Jihar Zamfara ta amince da ɗaukar ƙarin likitoci guda 50 domin inganta tsarin bayar da lafiya yadda ya dace da matakin gwamnatin tarayya a fannin kiwon lafiya.
Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dr. Nafisa Muhammad Maradun ta bayyana haka a lokacin da take bayyana buɗe wani taron ƙarawa juna ilimi na tsawon kwanaki huɗu ga masu kula da lafiya a Zamfara, wanda ma’aikatar lafiya ta jihar da ofishin haɗin gwiwa na SWAP suka shirya tare da hadin gwiwar ma’aikatar lafiya da jin daɗin jama’a ta tarayya (SCO) a yau Litinin.
A cewarta, gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin gwamna Dauda Lawal ta kuma amince da karɓar dukkanin masu aikin sa kai da ke aiki a dukkanin cibiyoyin kiwon lafiya na jihar zuwa ma’akatan dindindin.
Ta kuma bayyana cewa, gwamnatin jihar ta himmatu wajen inganta kasafin kuɗi a fannin kiwon lafiya domin inganta shi.
Dakta Nafisa ta bayyana taron bitar a matsayin wanda ya dace, inda ta ce za a horas da mahalarta bitar yadda za su iya tafiyar da harkokin kiwon lafiya cikin natsuwa da girmama alumma, musamman marasa lafiya a lokacin gudanar da aikin su.
Kwamishinan ta buƙaci mahalarta taron da su yi amfani da abin da suka koya yayin taron bitar domin inganta ayyukan bayar da lafiya a cibiyoyin kiwon lafiyar su a faɗin jihar.
A nasa jawabin, jami’in kula da SWAP a jihar Zamfara, Dakta Sani Abdullahi Wanzamai, ya ba da shawarar cewa ya kamata gwamnatin jihar ta mayar da hankali wajen gudanar da ayyukan inganta kiwon lafiya ta fannin horarwa da sake horar da ma’aikatan kiwon lafiya.
A cewarsa, ana iya bunƙasa ayyukan kiwon lafiya idan aka samu ingantaccen tsarin tattara bayanai don tantancewa da kuma rubutawa yadda ya kamata domin samun nagartattun hanyoyin kiwon lafiya a jihar ta Zamfara .
