Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da kwamitin ƙasa kan harkar ƙirƙira don inganta tattalin arzikin Najeriya

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani kwamiti na musamman da zai shirya taron ƙasa kan yadda za a haɓaka harkar ƙirƙira da nufin ƙara bunƙasa tattalin arzikin Najeriya. Ƙaddamarwar ta gudana ne ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, wanda ya ce wannan taro zai zama dandali na musayar dabaru da haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki a fannin ƙirƙira.

Kwamared Waiya ya bayyana cewa taron zai mayar da hankali wajen nuna irin basira da damar ƙirƙira da Kano ke da su, ciki har da kayayyakin gargajiya da al’adunmu. Haka kuma, za a samu wakilcin kafafen yaɗa labarai na ƙasa da ƙasa, tare da fitar da wata sanarwa mai ƙarfi da za ta jawo hankalin duniya kan muhimmancin wannan fanni.

Kwamishinan ya yabawa Gidauniyar Kannywood bisa wannan gagarumin shiri da ta bijiro da shi, yana mai cewa hakan ya dace da ƙudirin gwamnatin Jihar Kano na haɓaka tattalin arziki ta hanyar ƙirƙira da al’adu. Ya kuma gode wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa goyon bayansa na wannan taro, yana mai bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa.

Kwamitin wanda Kwamared Waiya ke jagoranta ya haɗa da kwamishinoni, masana, wakilan ƙungiyoyi daga ɓangarori daban-daban kamar harkar fina-finai, kayan sawa, adabi, da sauransu. Taron ana sa ran zai bai wa matasa da masu kirkira damar bunƙasa kasuwancinsu tare da samar da ayyukan yi ga al’umma.

By ukarofi