NSCDC a Katsina ta baza jami’ai 2807 domin tabbatar da tsaro a lokacin jana’izar Muhammadu Buhari

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar tsaro na Civil Defence a Katsina SC Buhari Hamisu ya sanar da haka ga manema labarai a Katsina.

Ya ce kwamandan hukumar Jihar Katsina Aminu Datti Ahmad ya faɗi haka a lokacin da yake taro da manyan jami’an sa.

Haka kuma Datti Ahamed ya bayyana cewa babban kwamandan na ƙasa Farfesa Ahmed Abubakar Audi ya kaɗu kwarai da ya sami labarin rasuwar shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari.

Babban kwamandan ya kuma umarci jami’an sa a jihar da su tabbatar da tsaro musamman a manyan wurare har zuwa lokacin da za’a gudanar da jana’izar marigayi.

“Wuraren kuwa sun haɗa da garin Daura da filin tashi da saukar jiragen sama na Umaru Musa Yar’adua a Katsina,”inji SC Buhari.

Sauran wuraren sun haɗa da fadar masu martaba sarakunan Katsina da Daura ya ce.

Shima kwamandan Datti Ahmad ya umarci jami’an tsaron a Ƙananan hukumomi 34 da ke jihar Katsina da su tabbatar da sun bada tsaro ga kaddarorin gwamnatin Ƙananan hukumomi da na jiha da ma na gwamnatin tarayya.

Ya ce dole ne su rinƙa sa ido da tattara bayanai na sirri da haɗa kai da sauran jami’an tsaro a jihar domin kare rayuka da dukiyar al’ummar jihar musamman manyan baƙin da za su shiga jihar.

Datti sai ya miƙa ta’aziyar babban kwamandan na ƙasa a madadin NSCDC ga iyalan marigayi Muhammadu Buhari, al’umma da gwamnatin Jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya kan babban rashi da akayi,yayi addu’ar Allah masa gafara, ya yafe masa kurakuransa.

By ukarofi