
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon shugaban mulkin soji a Nijeriya, Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa ya yi jinya a asibitin da Buhari ya rasu, inda ya bada ba’asin ganawarsu ta ƙarshe.
A ranar Lahadi ne Buhari, wanda ya mulki Nijeriya a matsayin soja a 1984 zuwa 1985 da matsayin farar hula a 2015 zuwa 2023, ya rasu, bayan shafe shekaru 82 a duniya.
Za a yi jana’izarsa ne a ranar Talata, 15 ga wata Yuli, 2025 da misalin ƙarfe 2 na rana a mahaifarsa dake Daura a Jihar Katsina.
A wata hira da gidan talabijin na Channels, Abdulsalami ya bayyana mutuwar tsohon shugaban ƙasar a matsayin babban rashi ga Nijeriya da ma shiyyar Afirka ta Yamma baki ɗaya.
Ya kuma ce, za a cigaba da tunawa da halin riƙon gaskiya da jajircewa da kishin ƙasa na marigayin.
Abdulsalami, wanda ya jagoranci shugabancin Nijeriya daga 1998 zuwa 1999, ya bayyana yadda alaƙarsa da Buhari ta samo asali tun a shekarar 1962 a lokacin da su biyun suka shiga aikin soja.
“Buhari ya kasance gaba da ni; kuma a lokacin yaƙin basasa, mun kasance muna yaƙi a rukuni ɗaya”, inji shi.
Ya kuma jinina wa halin tsayuwa akan gaskiya na marigayin, inda ya ce “za ka iya amincewa da Buhari akan komai a duniyar nan, kuma ba zai ha’ince ka ba.”
