NCAA ta dakatar da aiki da kamfanonin jiragen sama 11 kan basussuka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) ta umarci dukkan sassan gudanarwarta da su dakatar da bayar da ayyuka ga kamfanonin jiragen sama na cikin gida guda 11 bayan saka su cikin sabon jerin ‘Babu Biyan Kuɗi, Babu Aiki’ saboda bashin kuɗaɗen da suke bin hukumar.

Umarnin na ƙunshe ne cikin wata takardar cikin gida mai ɗauke da kwanan watan 22 ga Mayu, 2026.

A cewar takardar, an umurci dukkan sassan hukumar kula da harkokin jiragen sama da su dakatar da duk wata hidima ta gudanarwa da ta doka ga kamfanonin da abin ya shafa har sai sun biya bashin da ake binsu ko kuma sun cimma matsaya kan yadda za su biya bashin.

A tsakiyar rikicin akwai kuɗaɗen kaso biyar cikin ɗari na tikitin jirgi da kuma kuɗaɗen jigilar kaya ta jiragen sama, waɗanda kamfanonin jiragen sama ke karɓa a madadin NCAA domin tallafa wa sa ido kan tsaro, horas da ma’aikata da kuma kula da tattalin arzikin harkar sufurin jiragen sama a Nijeriya.

Takardar ta kuma umarci dukkan daraktocin NCAA da su dakatar da ayyuka ga kamfanonin da aka lissafa har sai Daraktan Kuɗi da Asusun Hukumar ya bayar da izinin ci gaba da hulɗa da su.

Daraktan Kuɗi da Asusun Hukumar, Olufemi Odukoya, ne ya sanya hannu a kan takardar, sannan aka aika da ita zuwa ofisoshin hukumar na shiyyoyi daban-daban. Haka kuma an aika kwafinta zuwa ga Darakta Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama da sauran manyan jami’ai.

Kamfanonin jiragen saman da abin ya shafa sun haɗa da Air Peace Limited, Ibom Air Limited, Arik Air Limited, United Nigeria Airlines, Umza Air, NG Eagle, Maɗ Air Limited, Caɓerton Helicopters, Oɓerland Airways, Rano Air da kuma ɓalueJet.

Takardar ta bayyana cewa: “Darakta Janar na Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ya bayar da umarni cewa babu wani sashe da zai bayar da hidima ga waɗannan kamfanonin jiragen sama ba tare da sahalewar sashen kuɗi da asusu ba.”

A ƙarƙashin wannan mataki, kamfanonin jiragen saman na iya fuskantar tangarɗa kai tsaye wajen samun tallafin gudanarwa daga hukumar, lamarin da ya haifar da damuwa tsakanin masu ruwa da tsaki, fasinjoji da sauran masu hulɗa da harkar sufurin jiragen sama kan yiwuwar samun tsaiko da rikice-rikicen aiki a ɓangaren.

By ukarofi

Leave a Reply