Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masu amfani da layukan sadarwa a Nijeriya sun sake samun damar cin gajiyar ayyukan aron katin waya na gaggawa bayan Hukumar Kare Gasa da Kare Haƙƙin Masu Saye ta Tarayya (FCCPC) ta dakatar da aiwatar da dokokinta na bayar da rancen kuɗi ta yanar gizo da hanyoyin zamani, wato Digital, Electronic, Online or Non-Traditional Consumer Lending (DEON) Regulations 2025.
Matakin ya biyo bayan umarnin da Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta bayar, inda ta umurci hukumar da ta dakatar da aiwatar da sabbin dokokin har sai an kammala shari’ar da ke ƙalubalantar ikon FCCPC na sa ido kan tsarin aron katin waya da kamfanonin sadarwa ke bayarwa.
A yayin da yake tabbatar da ci gaban, shugaban ƙungiyar Masu Samar da Sabis na Aikace-aikacen Wayar Sadarwa ta Nijeriya, wato Wireless Application Serɓice Proɓiders Association of Nigeria, Ayo Stuffman, ya ce an riga an dawo da sabis ɗin a kan layukan kamfanonin Airtel da Globacom.
Ana sa ran dawo da wannan sabis zai amfani miliyoyin masu amfani da wayoyin hannu da ke dogaro da aron kati domin sadarwa da kuma gudanar da ƙananan sana’o’i. Rahotanni sun nuna cewa kasuwar aron katin waya a Nijeriya na da kimar sama da naira biliyan 400 a duk shekara.
Tun farko dai FCCPC ta yi yunƙurin sanya tsarin aron katin waya ƙarƙashin sabbin dokokin bayar da rance ta yanar gizo, tana mai cewa an samu dubban ƙorafe-ƙorafe daga masu amfani da sabis dangane da matsalolin sirri da kuma wasu hanyoyin da ake zargin ba su dace ba wajen karɓar bashi.
Sai dai kafin hukumar ta ci gaba da aiwatar da dokokin, kotu ta shiga tsakani tare da bayar da umarnin dakatarwa har sai an yanke hukunci kan shari’ar da aka shigar.
Masu ruwa da tsaki a ɓangaren sadarwa sun bayyana cewa dakatar da dokokin na ɗan lokaci zai taimaka wajen dawo da sauƙin sadarwa ga masu amfani da layukan waya musamman waɗanda ke amfani da aron kati a matsayin hanyar ceto yayin ƙarewar kuɗin waya.
