NAHCON ta bai wa alhazai tabbacin dawo wa Nijeriya lafiya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Alhazai Ta ƙasa (NAHCON), ta buƙaci maniyyatan Nijeriya da su rungumi darussan sadaukarwa, tawali’u da haɗin kai yayin da suke gudanar da ibadar Ranar Arfa tare da miliyoyin Musulmi daga sassa daban-daban na duniya.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a wannan rana mai muhimmanci a aikin Hajji, ta bayyana Ranar Arfa a matsayin ƙololuwar ibadar Hajji kuma lokaci na neman rahama, gafara, addu’a da cikakken miƙa kai ga Allah Maɗaukakin Sarki.

Hukumar ta ce, ranar tana tunatar da Musulmi muhimmancin haƙuri, imani da sadaukarwa, tare da ba maniyyata damar yin nazari kan rayuwarsu, neman tuba da ƙara azama wajen aikata alheri da hidimtawa bil’adama.

NAHCON ta bayyana cewa darussan da aka koya daga yadda aka gudanar da aikin Hajji a shekarun baya ne suka taimaka wajen ci gaba da aiwatar da gyare-gyare domin ƙara inganta jin daɗi da walwalar maniyyatan Nijeriya da ke Saudiyya.

Hukumar ta ce tsarin gudanar da aikin Hajjin Nijeriya ya samu ci gaba sosai idan aka kwatanta da shekarun baya da maniyyata ke ɗaukar lokaci mai tsawo a sansanonin jirage suna jiran tashin jirgi zuwa ƙasa mai tsarki.

Sai dai duk da irin ci gaban da aka samu, hukumar ta amince cewa har yanzu akwai buƙatar ƙarin daidaito da inganta ayyukan hidima ga maniyyata.

“Darussan tarihi suna koya mana abubuwa masu muhimmanci. Idan muka kasa koyon darasi daga abubuwan da suka gabata, za mu iya sake fadawa cikin irin matsalolin baya. Amma idan muka yi nazari cikin hikima, za mu fi shirya gina kyakkyawar makoma,” inji sanarwar.

Hukumar ta kuma tabbatar wa maniyyata cewa za a sake duba matsalolin gudanarwa da aka gani a Hajjin bana domin gyara kura-kurai da ƙarfafa ayyukan Hajji a nan gaba.

NAHCON ta jaddada cewa an kafa ta ne domin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar harkokin gudanar da Hajji a Nijeriya, tana mai alƙawarin ci gaba da tafiya bisa manufofin waɗanda suka kafa ta.

A wani mataki na rage wa maniyyata nauyi, hukumar ta bayyana cewa ta samu nasarar sake tattaunawa kan kuɗin ciyarwa a Madina, inda ta ce kuɗaɗen da aka samu daga rangwamen za a mayar da su kai tsaye ga maniyyata.

Hukumar ta yabawa masu ruwa da tsaki, abokan hulɗa da maniyyata bisa goyon baya da fahimtar juna da suka nuna yayin gudanar da aikin Hajjin bana, tare da alƙawarin ci gaba da ƙoƙarin inganta ayyukanta.

NAHCON ta kuma yaba wa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa goyon baya da jagorancinsa wanda ta ce ya taimaka wajen nasarorin da aka samu a jigilar maniyyata da gudanar da Hajjin 2026.

Haka kuma ta yabawa Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, bisa jagoranci da tabbatar da aiwatar da manufofin da suka dace wajen gudanar da aikin Hajji.

Hukumar ta kuma yaba wa ma’aikata da shugabannin NAHCON bisa ƙwazon da suka nuna wajen sauya ƙalubalen gudanarwa zuwa nasarori a aikin Hajjin bana.

A ƙarshe, NAHCON ta bai wa maniyyatan Najeriya tabbacin cewa an ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da dawowarsu gida cikin aminci, tsari da sauƙi bayan kammala ibadun Hajji.

Hukumar ta yi addu’ar Allah Ya karɓi addu’o’i da ibadun maniyyata, tare da kira ga ’yan Nijeriya da su fifita haɗin kai da hikima maimakon rarrabuwar kai da fusata.

“Allah Ya bai wa dukkan maniyyata Hajji lada tare da dawo da su gida lafiya zuwa iyalansu da al’ummominsu,” inji sanarwar.

By ukarofi

Leave a Reply