Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wani ɗan asalin jihar Borno mai suna Enoch Yohanna ya tayar da ƙura bayan ya zargi Gwamnatin Tarayyar Nijeriya da bai wa tsofaffin mayaƙan Boko Haram da suka tuba kuɗaɗe har Naira miliyan uku bayan kammala shirin gyaran hali.
Yohanna ya yi wannan zargi ne yayin wani taron jama’a, inda ya bayyana takaicinsa kan abin da ya kira amfani da kuɗin harajin jama’a wajen tallafa wa mutanen da ake zargi da hannu a kashe-kashe da sace-sacen jama’a a yankin Arewa maso Gabas.
A cewarsa, “Abin da ke ƙona min rai shi ne mutanen da suka kashe mahaifina da kuma waɗanda suka yi garkuwa da mutane ana ba su kuɗi daga harajin da jama’a ke biya.”
Rahoton ya danganta zargin ne da shirin Operation Safe Corridor, wanda gwamnatin tsohon Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ta ƙaddamar a shekarar 2016 domin samar da hanyar ficewa daga ta’addanci ga mayaƙan da suka miƙa wuya.
An tsara shirin ne domin gyaran tunani, horaswa da sake haɗa tsofaffin mayaƙa cikin al’umma ta hanyar tsarin kawar da tsattsauran ra’ayi, gyaran hali da sake tsugunarwa.
Yohanna ya yi iƙirarin cewa ana rarraba tsofaffin mayaƙan ne bisa irin laifuffukan da suka aikata kafin a ba su horo da kuɗaɗen tallafi.
Ya ce wasu daga cikinsu na karɓar naira miliyan uku bayan sun kammala shirin, tare da albashin wata-wata da ya ce ya kai naira dubu 50.
Har ila yau, ya yi zargin cewa wasu daga cikin waɗanda suka tuba ana haɗa su da ƙungiyoyin sa-kai na tsaro na Ciɓilian JTF, yayin da wasu kuma ake tura su zuwa wasu ƙasashe domin aikin haƙar ma’adanai.
Yohanna ya kuma bayyana cewa akwai waɗanda ke rayuwa cikin walwala tare da motocin alfarma da masu tsaro duk da zargin hannu a munanan hare-hare.
Sai dai babu wata sanarwa daga Gwamnatin Tarayya ko hukumomin tsaro da ta tabbatar da waɗannan zarge-zarge a lokacin haɗa wannan rahoto.
Maganganun nasa dai sun sake tayar da muhawara kan yadda ake tafiyar da shirin gyaran hali da sake haɗa tsofaffin mayaƙan Boko Haram cikin al’umma, musamman daga iyalan waɗanda rikicin ya shafa kai tsaye.
