Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa, kimanin ’yan Nijeriya miliyan 35 na fuskantar matsananciyar yunwa daga watan Yuni zuwa Agusta na shekarar 2026, sakamakon ƙara ta’azzarar matsalar rashin abinci a ƙasar.
Rahoton da ƙungiyar Haɗin Gwiwar Jinƙai ta Majalisar ɗinkin Duniya ta fitar ya bayyana cewa Nijeriya na cikin ƙasashen da ke fuskantar babbar matsalar abinci a duniya, inda aka ce kusan ɗaya cikin mutane bakwai za su shiga yanayin ƙarancin abinci mai tsanani a lokacin damina.
Majalisar ta ce, wannan yanayi zai fi tsanani a yankunan Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, inda aka kiyasta cewa sama da yara miliyan 6.4 za su iya fuskantar matsananciyar rashin abinci mai gina jiki a cikin shekarar nan.
A cikin rahoton da aka fitar ranar Juma’a 22 ga Mayu, 2026, hukumar ta bayyana cewa idan ba a gaggauta bada tallafin jinƙai ba, miliyoyin iyalai za su shiga mummunan hali da zai tilasta musu rage yawan abinci, sayar da kadarori, ko kuma fitar da ‘ya’yansu daga makaranta — matakan da ke da tasiri na dogon lokaci ga ci gaban ƙasa.
Majalisar ta kuma yi kira ga ƙasashen duniya da masu bayar da tallafi da su gaggauta taimakawa Nijeriya, domin dakile yaɗuwar wannan matsala da ke ƙara ƙamari.
Rahoton ya kuma bayyana cewa shirin jinƙai na shekarar 2026 da aka tsara da kimanin dala miliyan 516 ya samu ƙarancin kuɗi, inda zuwa yanzu aka tara kusan dala miliyan 215 kacal, wanda ya yi ƙasa da kashi 50 cikin ɗari na abin da ake buƙata.
Masana sun bayyana cewa wannan ƙarancin kuɗin na iya ƙara jefa miliyoyin mutane cikin mawuyacin hali idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba.
