Daga USMAN KAROFI
Hukumar kula da cututtuka masu yaɗuwa ta ƙasa (NCDC) ta bayyana cewa an samu raguwar sabbin masu kamuwa da cutar Lassa a mako na 19 na shekarar 2026. A cewar rahoton hukumar, adadin waɗanda aka tabbatar sun kamu ya ragu daga mutum 22 a makon da ya gabata zuwa mutum 17, inda aka samu sabbin masu ɗauke da cutar a jihohin Ondo, Bauchi, Edo, Kogi, Taraba da Nasarawa.
Sai dai duk da wannan raguwar, NCDC ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar ya kai 204 tun daga farkon shekarar 2026. Hukumar ta bayyana cewa kaso 25.7 cikin 100 na waɗanda suka kamu sun mutu, adadi da ya fi na makamancin lokacin a shekarar 2025 wanda ya kasance kaso 19.4 cikin 100.
Rahoton ya nuna cewa jihohi 23 da ƙananan hukumomi 108 sun riga sun samu aƙalla mutum guda da aka tabbatar ya kamu da cutar a bana. Haka kuma, kashi 84 cikin 100 na dukkan waɗanda suka kamu sun fito ne daga jihohi biyar da suka hada da Bauchi, Ondo, Taraba, Edo da Benuwai, lamarin da ke nuna yadda cutar ta fi ƙamari a wasu yankuna na ƙasar.
NCDC ta ce tana ci gaba da aiwatar da matakan daƙile yaɗuwar cutar, ciki har da ƙarfafa sa ido, horas da ma’aikatan lafiya, wayar da kan al’umma da kuma inganta kula da marasa lafiya. Hukumar ta kuma bayyana cewa an samu kamuwar wani ma’aikacin lafiya da cutar a cikin makon rahoton, abin da ke nuna ci gaba da kasancewar haɗari ga masu aikin jinya da lafiya.
