Cire tallafin mai ya ceto Nijeriya daga talaucewa – Tinubu

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi ya ceci Najeriya daga faɗawa cikin matsanancin taɓarɓarewar tattalin arziki. Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi baƙuncin gwamnonin jihohi da suka kai masa ziyara domin taya shi murnar Sallah da kuma cika shekaru uku da hawansa mulki.

Shugaban ya amince cewa matakin cire tallafin ya jawo wa ‘yan Najeriya wahalhalu a farko, amma ya ce hakan ya zama dole domin daƙile durƙushewar tattalin arzikin ƙasar. A cewarsa, an shafe shekaru ana kashe makudan kuɗaɗe wajen biyan tallafin da ba ya amfani ga mafi yawan jama’a, maimakon saka hannun jari a ɓangarorin da za su bunƙasa tattalin arziki.

Tinubu ya ce a yanzu alamomin tattalin arziki na nuna farfaɗowa, inda ya bayyana cewa noma, gine-ginen hanyoyi da sauran ayyukan more rayuwa na samun ci gaba.

Ya kuma yaba wa gwamnonin jihohi bisa goyon bayan da suka ba gwamnatinsa wajen shawo kan jama’a su yi haƙuri da sauye-sauyen tattalin arzikin da ake aiwatarwa.

A nasa ɓangaren, shugaban ƙungiyar gwamnonin Najeriya kuma gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya ce cire tallafin man fetur ya ƙara wa jihohi kuɗaɗen shiga, wanda ya ba su damar biyan albashi, fansho da aiwatar da muhimman ayyukan raya ƙasa. Ya kuma buƙaci shugaban ƙasa ya yi la’akari da ƙara mafi karancin albashi zuwa naira dubu 100,000 domin inganta rayuwar ma’aikata.

By ukarofi

Leave a Reply