
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Litinin tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Ebele Johnathan da tsohon shugaban ƙasar Ghana, Nana Akufo-Addo suka ziyarci Kashim Shettima da tawagarsa a Landon a yayin jimamin rasuwar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Mai taimaka wa Mataimakin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya bayyana hakan a wata takarda.
Ya ce, iyalan marigayin sun shaida cewa ya rasu ne bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci, da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Lahadi, a wani asibiti dake Landon.
A ranar 28 ga watan Yuni ne marigayin ya yi tafiya domin duba lafiyarsa, inda a makon da ya gabata kuma jikin nasa ya yi tsanani.
Tuni Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin a yi ƙasa-ƙasa da tutocin Nijeriya a faɗin ƙasar da sanar da jimamin mako guda a sakamakon rashin tsohon shugaban.
Shettima tare da ƴan tawagarsa a halin yanzu yana Landon bisa umarnin Shugaba Tinubu domin ya rako gawar marigayin zuwa gida Nijeriya
