Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya bai wa kowane mahajjacin jihar kyautar Riyal 300 na Saudiyya yayin da ya kai musu ziyara a sansanoninsu da ke Mina a daren Alhamis.
A cewar sanarwar da mai bai wa gwamna shawara kan harkokin yaɗa labarai, Malam Ibraheem Musa, ya fitar, kowanne mahajjaci zai karɓi kusan Naira 114,000 bisa farashin canjin kuɗi na yanzu.
Gwamnan ya yaba da ɗabi’a da jajircewar alhazan Kaduna tare da jinjinawa hukumar jin daɗin alhazai ta Jihar Kaduna bisa nasarar gudanar da aikin Hajjin bana. Haka kuma ya yaba wa kwamitin tawagar Hajji na jihar ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abubakar Mustapha saboda yadda suka tabbatar da gudanar da aikin cikin nasara.
Uba Sani ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarar aikin Hajjin bana, tare da neman afuwar duk wata ƙaramar matsala da ka iya tasowa yayin gudanar da aikin.
Ya kuma buƙaci alhazan su ci gaba da yi wa Najeriya da Jihar Kaduna addu’ar zaman lafiya, yana mai cewa ci gaba ba zai samu ba idan babu zaman lafiya.
A nasa jawabin, shugaban hukumar hin daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, Malam Salihu S. Abubakar, ya gode wa gwamnan bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar domin inganta walwalar alhazai.
Shi ma babban mai binciken kuɗaɗe na Jihar Kaduna, Alhaji Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa tun daga shekarar 1999 babu wani gwamnan Kaduna da ya kai wa alhazai ziyara a sansanoninsu kamar yadda Gwamna Uba Sani ya yi.
Wannan mataki na gwamnan ya jawo farin ciki da yaba wa daga alhazan Kaduna, waɗanda suka yi masa addu’ar samun nasara da ci gaba da kawo ci gaba a jihar.
