Daga USMAN KAROFI
Gwamnonin Najeriya a ƙarƙashin ƙungiyar Nigeria Governors’ Forum (NGF) sun yi kira ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya yi la’akari da ƙarin mafi ƙarancin albashi zuwa N100,000. Sun ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin tarayya ta yi, musamman cire tallafin mai, sun ƙara yawan kuɗaɗen da jihohi ke samu, wanda ke ba su damar biyan basussuka da gudanar da ayyuka.
Shugaban NGF kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya ce jihohi da dama a baya sun dogara ne da rance da kuma sayen bashi domin tafiyar da harkokinsu, amma yanzu yanayin ya sauya. Ya bayyana cewa yawancin jihohi sun fara rage bashi kuma suna da karfin biyan albashi da gudanar da manyan ayyukan ci gaba.
A nasa bangaren, Shugaba Bola Tinubu ya kare matakin cire tallafin mai, inda ya ce matakin mai wahala ne amma ya ceci Najeriya daga durƙushewar tattalin arziki. Ya ce sauye-sauyen sun fara dawo da daidaito a tattalin arziki, tare da haɓaka noma, gine-gine da sauran fannoni masu muhimmanci ga ci gaban ƙasa.
Haka kuma, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima da wasu gwamnoni sun goyi bayan matakan, suna cewa suna fara ganin ribar sauye-sauyen. Sun buƙaci haɗin kai da haƙuri daga ‘yan Najeriya yayin da gwamnati ke ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen da nufin inganta rayuwar jama’a da samar da ci gaba mai ɗorewa.
