Mutane uku sun rasu sakamakon faɗawa cikin rijiya a Kano

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane uku sakamakon faɗawa cikin rijiyoyi daban-daban a lokuta daban a ranar Juma’a. Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi, ya ce an samu kiran gaggawa da safiyar ranar, inda aka garzaya domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su.

A cewar hukumar, an fara samun rahoton mutuwar wani namiji da ba a san ko wane ne ba a unguwar Semegu da ke ƙaramar hukumar Kumbotso. An ce jami’an ceto sun ciro gawarsa daga cikin rijiya tare da mika ta ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike kan musabbabin faruwar lamarin.

A wani lamari makamancin haka, wata mata mai shekaru 32, Maimuna Shitu, tare da jaririnta mai watanni 18 mai suna Harisu Muntari, sun fada cikin rijiya a kauyen Madarin Taba da ke karamar hukumar Warawa. Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne yayin da matar ke fama da matsalar tabin hankali kafin su faɗa cikin rijiya.

Hukumar kashe gobarar ta ce ta miƙa gawarwakin waɗanda lamarin ya rutsa da su ga shugabannin unguwa da kuma iyalan mamatan, tare da bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan musabbabin haɗurran. Ta kuma yi kira ga al’umma da su rika rufe rijiyoyi yadda ya kamata domin kauce wa sake faruwar irin wannan iftila’i.

By ukarofi

Leave a Reply