Liverpool ta sallami Arne Slot

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Liverpool ta sallami kocinta, Arne Slot, bayan ya shafe shekaru biyu yana jagorantar ƙungiyar. Rahotanni sun bayyana cewa an ɗauki matakin ne sakamakon rashin kyakkyawan sakamako a kakarsa ta biyu, duk da cewa ya lashe gasar firimiya a shekararsa ta farko.

Arne Slot, mai shekaru 47, ya jagoranci Liverpool zuwa lashe kofin gasar lig na 20 a kakarsa ta farko, abin da ya ƙara masa suna a cikin kwallon kafa ta Ingila. Sai dai a kakarsa ta biyu, ƙungiyar ta fuskanci matsaloli da suka kai ta kammala kakar a mataki na biyar a teburin firimiya.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon kocin Bournemouth, Andoni Iraola, shi ne ke kan gaba wajen maye gurbin Slot a matsayin sabon kocin Liverpool. Wannan na zuwa ne yayin da ƙungiyar ke neman dawo da martabarta a gasar gida da ta nahiyar Turai.

Kungiyar ta Fenway Sports Group, wadda ke mallakar Liverpool, ta bayyana godiyarta ga gudunmawar da Slot ya bayar, tana mai cewa ya kasance jagora mai ƙwazo da ƙwarewa. Ta ce duk da matakin da aka ɗauka, ba za su manta da nasarorin da ya kawo wa ƙungiyar ba.

By ukarofi

Leave a Reply