Tsagin Turaki na PDP ya bayyana Jonathan a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na 2027

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Wata ɓangare na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2027, duk da cewa bai halarci taron ba. An amince da takarar Jonathan ne a wani babban taro na musamman da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin ɓangaren Kabiru Turaki.

Rahotanni sun bayyana cewa an miƙa takardar tabbatar da takararsa ga ɗan majalisar wakilai daga jihar Bayelsa, Fred Agbedi, wanda ya karɓe a madadin Jonathan. Wannan mataki ya biyo bayan rikicin cikin gida da ke ci gaba da raba jam’iyyar zuwa ɓangarori daban-daban, musamman tsakanin ɓangaren Turaki da kuma ɓangaren da ke da alaƙa da Nyesom Wike.

An shirya gudanar da taron a A-Class Park and Event Centre da ke Abuja, amma daga bisani an tilasta mayar da shi zuwa ofishin ɓangaren jam’iyyar da ke Area 10, Garki, bayan hukumomi sun gargaɗi masu gudanar da taron da su yi aiki da shugabancin PDP da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta amince da shi.

Sai dai ɓangaren Wike ya ce wannan taro ba shi da sahalewa kuma ba ya wakiltar jam’iyyar PDP ta gaskiya. Lamarin ya ƙara nuna irin rarrabuwar kai da ke addabar jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027, yayin da ake ci gaba da taƙaddama kan sahihancin shugabanci da tikitin takara.

By ukarofi

Leave a Reply