An kama wasu da ake zargi da garkuwa da mutane a Ogun

Spread the love

Daga USMAN KAROFI

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta sanar da samun gagarumar nasara a yaƙi da masu garkuwa da mutane bayan kama wasu da ake zargi da hannu a hare-haren satar mutane da suka addabi yankuna daban-daban na jihar. Binciken da jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane suka gudanar ya kai ga kama Muhammadu Abdullai mai shekaru 67, wanda ke riƙe da sarautar Seriki Fulani na Ijebu-Ode.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an gano wata jaka da aka yi amfani da ita wajen kai kuɗin fansa ga masu garkuwa da mutane a cikin harabar gidan iyalan wanda ake zargi. Binciken ya biyo bayan jerin sace-sacen mutane da aka samu a yankunan Ijebu-Ode, Imodi, Irewon, Iwode, Okun-Owa da sauran al’ummomin da ke maƙwabtaka da su.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun danganta ayyukan ƙungiyar da wani da ake kira Bala Muhammadu, wanda kwanan nan ya kammala zaman gidan yari na shekaru biyar bisa laifukan da suka shafi garkuwa da mutane.

Sai dai kafin jami’an tsaro su kai ga cafke shi, an ce wani yaro a gidan ya hango ‘yan sanda tare da sanar da shi da wasu ‘yan uwansa biyu, lamarin da ya ba su damar tserewa ta cikin daji.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Olubode Ojajuni, ya yaba wa jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai cewa nasarar ta samo asali ne daga tattara bayanan sirri da kuma sa ido na musamman.

Ya tabbatar da cewa bincike na ci gaba domin cafke sauran waɗanda suka tsere tare da rusa gaba ɗaya cibiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar jihar da yankunan da ke maƙwabtaka da ita.

By ukarofi

Leave a Reply