Daga SHAFII SANI MOHAMMED
Wata tawaga daga Majalisar Tarayya wadda ke da alhakin sa ido kan hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta gudanar da ziyarar duba tantunan maniyatan Najeriya a Mina, a matsayin wani ɓangare na tantance yadda aikin Hajjin shekarar 2026 ke gudana.
Wannan ziyarar sa ido ta kasance cikin hurumin doka na majalisar domin sa ido kan yadda ake tafiyar da aikin Hajji tare da tabbatar da cewa maniyatan Najeriya na samun ingantaccen kulawa da ayyuka masu inganci a tsawon zamansu a ƙasar Saudiyya.
A yayin ziyarar, tawagar ta duba wasu tantuna na jihohin Najeriya inda ta gana da maniyata da jami’an da ke kula da jin daɗin su. A yayin wannan tattaunawa, masu kula da alhazai daga jihohi da kuma maniyata sun bayyana gamsuwarsu da ayyukan da NAHCON ke gudanarwa, musamman a ɓangaren masauki da abinci.
Maniyatan sun yaba da inganci da daidaiton abincin da ake ba su a tsawon zamansu a Mina. Sai dai sun roƙi a ƙara shigar da nau’ikan abincin gargajiya na Najeriya a ayyukan Hajji na gaba, inda suka bayyana cewa wasu tsofaffin alhazai na samun wahalar daidaitawa da wasu irin abincin da ake bayarwa.
Haka kuma maniyatan sun jawo hankali kan buƙatar ƙarin banɗakuna a cikin sansanonin, inda suka ce waɗanda ake da su yanzu na yawan haifar da dogayen layi, musamman a lokutan cunkoso. Sun roƙi hukumomi da su ƙara yawan waɗannan wurare domin inganta jin dadi, sauƙaƙa al’amura da kuma tsafta.
Bugu da ƙari, maniyatan sun nuna godiya mai yawa ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa kulawarsa ga jin daɗin maniyatan Najeriya da kuma goyon bayan da ake bayarwa wajen tabbatar da nasarar aikin Hajji. Sun kuma miƙa godiya ga tawagar majalisar bisa wannan ziyara da suka yi domin duba halin da suke ciki da kuma matsalolinsu.
Da yake jawabi yayin ziyarar, shugaban tawagar, Sanata Ali Ndume, ya buƙaci maniyata da su ci gaba da yin addu’o’i na zaman lafiya, tsaro, kwanciyar hankali da ci gaban Najeriya. Ya kuma buƙace su da su tuna da shugabanni, iyalansu da sauran ‘yan ƙasa yayin gudanar da ibadar Hajji.
Sanata Ndume ya tabbatar wa maniyata cewa dukkanin bayanai da ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar za a rubuta su tare da duba su yadda ya kamata. Ya bayyana cewa wasu daga cikin matsalolin na ƙarƙashin ikon hukumar alhazai ta jiha da gwamnatocin jihohi, yayin da waɗanda suka shafi NAHCON kai tsaye za a shigar da su cikin rahoton kwamitin sa ido.
Haka kuma shugaban kwamitin majalisar wakilai kan Hajj da Umrah, Honarabul Ja’afar Mohammed, ya sake tabbatar da ƙudirin majalisar da gwamnatin tarayya wajen tabbatar da jin daɗin maniyatan Najeriya. Ya ce za a duba dukkan ƙorafe-ƙorafen da aka gabatar a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin inganta harkokin Hajji da ƙara ingancin ayyuka.
Ya kuma ƙarfafa wa maniyata gwiwa da su ci gaba da addu’o’i ga haɗin kan Najeriya, zaman lafiya da ci gaban ƙasa, da kuma yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu da iyalansa addu’a.
Shafii ya ruwaito daga Mina, Saudi Arabia.
