Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Hukumar Hisbah a ƙaramar hukumar Nasarawa da ke Jihar Kano ta gudanar da sumame a kasuwar Dakata, inda ta kama wasu tsofaffi a cikin shagunan caca na LOTO. Sumamen ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin OC Patrol na hukumar, Muhdeen Isah, kuma ya mayar da hankali ne kan daƙile ayyukan da suka saɓa wa addini da tarbiyya.
A yayin sumamen, an kama wasu tsofaffi da suka tsunduma cikin cacar, lamarin da Hisbah ta bayyana a matsayin abin takaici. Jami’an Hisbah sun yi wa waɗanda aka kama nasiha, suna mai jaddada cewa ya kamata su karkata rayuwarsu zuwa ibada da tunani mai amfani, maimakon shiga harkar da bata da amfani ga rayuwa da lahira.
Daga cikin waɗanda aka kama, wasu sun bayyana jin daɗin yadda aka yi musu nasiha cikin natsuwa da ladabi. Sun amince da kuskuren da suka aikata tare da bayyana aniyar sauya hali, su rungumi hanyar da ta dace da koyarwar addini da ɗabi’a ta gari.
