Daga UMAR GARBA a Katsina
Gawar tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta baro birnin Landan, Birtaniya, da safiyar yau Talata, zuwa garin Daura a Jihar Katsina, domin gudanar da jana’izar sa.
Jaridar PUNCH Online ta ruwaito cewa an ɗauko gawar tsohon shugaban ƙasar ne a jirgin saman Najeriya.
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ne ke jagorantar tawagar gwamnatin tarayya da shirye-shiryen dawo da gawar tsohon shugaban ƙasar zuwa gida.
A jiya Litinin, Blueprint Manhaja ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai karɓi gawar tsohon shugaban ƙasar a Katsina kafin a kai ta Daura domin rufewa.
Ministan watsa labarai da tsare-tsaren na ƙasa, Mohammed Idris, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Abuja.
