Yadda babbar ƴar Buhari, Fatima ta fashe da kuka yayin da suka isa wajen jana’iza

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ana cigaba da jimamin rashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a yau Talata, yayin da iyalansa ƙarƙashin jagorancin Fatima Buhari suka je wajen jana’izar a Daura.

An ga yadda Fatima ke zubar da ƙwalla a lokacin da ta isa gidansa dake garin, inda a nan ne za a yi jana’izar.

Haka kuma an ga yadda makusantanta suke lallashin ta yayin da suke tarbar su.

Sannan, gabannin haka ne sauran iyalan suka isa birnin domin gudanar da shirye-shiryen jana’izar.

A safiyar yau ne gawar ta bar Landon zuwa Nijeriya, wadda za a yi jana’izarta da misalin ƙarfe 2 na rana.

By Babaji