Wanda ya yi yunƙurin kashe ni ya tafi ya bar ni a raye – Sunday Igboho kan rasuwar Buhari

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mai fafutukar kafa ƙasar Yarbawa, Sunday Adeniyi da aka fi sani da Sunday Igboho ya magantu game da rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana a matsayin “babban mai laifi” da ya taɓa yunƙurin halaka shi.

A ranar Lahadi ne shugaban Nijeriyar ya rasu a wani asibiti dake Landon bayan wani gajeren rashin lafiya.

A wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa, an ga yadda Igboho ya ke bayanin yadda tsohon shugaban ƙasar ya umarci jami’an DSS su je gidansa da tsakar dare.

Ya yi ikirarin cewa an yi hakan ne da nufin fitar da shi waje bayan Buhari ya haɗa kai da wasu ƴan ƙabilar Yarbawa.

“Mutane na, ya kamata mu ɗauki darasi daga wannan. Mutumin, Muhammadu Buhari, ya rasu, amma ina raye a yau. Ina godiya ga Ubangiji kan tsare rayuwata”, inji Igboho.

A ranar 1 ga watan Yuli, 2021 ne jami’an DSS suka kai samame gidan Igboho dake Ibadan, inda suka kashe makusantansa biyu tare da yin awon gaba da wasu guda 12.

Sannan, an yi ruwan alburusai ga motoci masu alfarma dake gidan, inda daga lokacin ne hukumar DSS ta ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa-a-jallo.

By Babaji