
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gidauniyar abokai ta ‘C&C Friends Foundation’ ta bayyana kaɗuwarta game da rashin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar Lahadin da ta gabata.
Marigayin, ya rasu ne a wani asibiti dake Landon bayan shafe shekaru 82 a duniya.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta na ƙasa, Sanusi Garba Kalambaina, gidauniyar ta miƙa gaisuwar ta’aziyyarta ga Shugaba Bola Tinubu, iyalan marigayin, gwamnatin Katsina da al’ummarta gami da ilahirin ƴan Nijeriya.
Ta kuma yaba wa jajircewa da ƙoƙarinsa wajen samar wa Nijeriya ci-gaba a fannoni da dama tare da fatan samun haƙurin juriyan rahsin sa ga ƴan uwa da abokan arziƙi.
Kazalika, ta yi masa fatan samun rahamar Allah da addu’ar ya kasance ɗaya daga cikin ƴan Aljanna.
