An yi jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Daura

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Imam Hassan Yusuf na babban masallacin garin Daura ya jagoranci Sallar jana’izar a filin jiragen sama na Choppers da misalin ƙarfe 4:56 na yamma.

Gwamnatin Katsina ta gina wannan filin ne a lokacin da marigayi Muhammadu Buhari ke shugaban kasa.

Tun da misalin ƙarfe goma na safe jama’a musamman ƴan yankin Daura da manyan baƙi daga sassa daban-daban suka fara tururuwa zuwa gidan marigayi Muhammadu Buhari, inda wasu kuma suka isa filin da aka gudanar da jana’izar.

Shugaba Bola Ahmad Tinubu wanda ya samu rakiyar ɗansa Seyi Tinubu da Gwamna Dikko Raɗɗa suka tarbi gawar marigayi Muhammadu Buhari a Filin jirgin sama na Umar Musa Yar’adua.

Haka kuma a tawagar shugaban ƙasa akwai ministoci da manyan jami’an gwamnati da na tsaro, mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, kakakin majalisar wakilai da sauran ƴan Majalisar Dokoki na kasa.

Akwai kuma tsoffin mataimakan shugaban ƙasa Atiku Abubakar da Yemi Osibanji da tsaffin gwamnoni na da da na yanzu kusan su 20.

Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shattima da shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Nijeriya, Femi Gbajabiamila, uwargidan tsohon shugaban ƙasar A’isha Buhari da Yusuf Buhari babban ɗa ga marigayi Muhammadu Buhari suka iso da gawar zuwa Nijeriya daga.

Haka kuma akwai uwargidan shugaban ƙasa Remi Tinubu da wasu matan gwamnoni.

Tun jiya dai sarkin musulmi Sultan Sa’ad Abubakar ya isa garin Daura da tsohon gwamnan Kaduna malam Nasiru El-rufa’i da tsoron gwamnan Rivers wanda harwala yau tsohon ministan sufuri Rotimi Ameachi da tsohon ministan Shari’a malami SAN da Farfesa Sheikh Ali pantami

By Babaji