Daga UMAR GARBA a Katsina
Gawar marigayi tsohon shugaban ƙasar Nijeriya, Muhammadu Buhari ta isa Katsina tare da rakiyar mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima a filin jirgin sama na Umaru Musa YarAdua, dake Katsina.
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya tarbi gawar a filin jirgi na Katsina, yanzu haka ana shirin wucewa da gawar zuwa mahaifar marigayin wato garin Daura don gudanar da sallar jana’iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Marigayi shugaba Muhammadu Buhari ya rasu ne a ranar 13 ga watan Yulin 2025 a wani asibiti da ke Landan bayan rashin lafiya.

