Daga USMAN KAROFI a Abuja
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya shigar da ƙara gaban kotun ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin da babbar kotun tarayya dake Abuja ta yanke, wanda ta umarci dawo da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan zuwa majalisa bayan dakatarwar da aka yi mata.
Sanarwar ɗaukaka ƙarar, wacce aka rubuta a ranar 14 ga Yuli, 2025, ta shigo ne daga sashen Abuja na kotun ɗaukaka ƙara.
Akpabio yana ƙalubalantar hukuncin da Mai Shari’a Binta Nyako ta yanke a ranar 4 ga Yuli, inda ta bayyana dakatarwar watanni shida da aka yi wa Akpoti-Uduaghan a matsayin wuce gona da iri kuma saɓawa haƙƙin wakilcin da mutanen mazaɓar ta ke da shi. Kotun ta amince cewa majalisar tana da ikon ladabtar da mambobinta, amma ta ce nau’i da tsawon dakatarwar sun yi yawa. Haka kuma, an ci tarar Sanata Natasha Naira miliyan biyar saboda wani rubutu mai barkwanci da ta wallafa a Facebook lokacin shari’ar, wanda aka ce ya saɓa da umarnin kotu.
A nata ɓangaren, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar da ɗaukaka ƙarar nata, tana ƙalubalantar hukuncin raini da kotun ta yanke, inda ta ce kotun ba ta da hurumin sauraron irin wannan ƙara da ya shafi abin da ya faru a wajen zaman kotu.
Haka zalika, lauyoyin Akpabio sun gabatar da ƙarar suka ce batun yana cikin harkokin cikin gida na majalisa, wanda ba aikin kotu ba ne bisa sashe na 251 na kundin tsarin mulki na 1999.
A cikin ƙarar ɗaukaka ƙara da ke ƙunshe da hujjoji 11, Akpabio ya soki kotun da ta yi watsi da ƙorafinsa na farko, sannan ta yanke hukunci da ke tsoma baki cikin ikon ‘yan majalisa na gudanar da harkokinsu. Ya ƙara da cewa dakatarwa, muhawara a zauren majalisa, da ƙudurori da ake ɗauka ba sa cikin abubuwan da kotu ke da hurumi a kansu. Haka kuma, ya ce Sanata Natasha ba ta bi hanyoyin cikin gida na warware saɓani ba, musamman kwamitin ladabtarwa da haƙƙoki na majalisa, kamar yadda dokokin majalisar dattawa suka tanada.
